Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bukaci Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, da ya sauya manufofinsa na tattalin arziki ko kuma ya sauka daga mulki, tana mai zargin cewa matakan gwamnatin sun jefa miliyoyin ‘yan Nijeriya cikin talauci da yunwa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar, Malam Bolaji Abdullahi, ya fitar ranar Asabar. Ya ce ADC ta damu da rahoton Bankin Duniya da ya nuna mutum miliyan 139 a Nijeriya na rayuwa cikin talauci, da kuma rahoton Hukumar Abinci ta Duniya (WFP) da ya ce mutum miliyan 17 na fama da matsananciyar yunwa.
Jam’iyyar ta ce wadannan alkaluma na nuna cewa manufofin tattalin arzikin gwamnatin APC sun gaza, kuma idan aka ci gaba da su bayan zaben 2027, za su iya jefa kasar cikin mawuyacin hali.
“Manufofin Tinubu sun fifita samar wa gwamnati kudi fiye da rayuwar jama’a”
ADC ta ce ta dade tana gargadin cewa karin kudaden shiga da gwamnati ke yabawa ba su da amfani idan ba su inganta rayuwar jama’a ba.
Jam’iyyar ta ce gwamnatin Tinubu ta ci gaba da kare manufofinta duk da halin da mutane ke ciki, tana mai cewa abin da gwamnati ke kira “sadaukarwa mai dole” ya kara jefa jama’a cikin wahala.
Ta kara da cewa shekaru uku bayan fara aiwatar da manufofin, yanzu an ga sakamakonsu, inda miliyoyin mutane ke fama da talauci da yunwa.
Jam’iyyar ta ce gwamnatin da Nijeriya ke bukata ita ce wadda za ta fifita jin dadin jama’a, ba wai kididdigar tattalin arziki kadai ba.
A cewarta, ba za a kawar da talauci da rabon tallafi kawai ba, sai an gina tattalin arzikin da zai bai wa jama’a damar samar da abinci, samun aikin yi da rayuwa mai inganci.
ADC ta ce idan aka zabe ta, za ta rage tsadar makamashi domin saukaka samar da abinci.
Ta kuma yi alkawarin inganta tsaron yankunan noma da hanyoyin sufuri domin manoma su koma gonakinsu ba tare da fargaba ba.
Jam’iyyar ta ce za ta gyara madatsun ruwa 264 da aka yi watsi da su domin fadada noman rani, tare da samar da ingantattun iri, taki, ayyukan fadakarwa ga manoma da kuma wuraren adana da sarrafa amfanin gona domin rage asarar bayan girbi.
