DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasa'A shirye nake in rasa raina wajen kare kuri'ata a 2027'

‘A shirye nake in rasa raina wajen kare kuri’ata a 2027’

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa a shirye yake ya rasa ransa wajen kare ƙuri’unsa a babban zaɓen 2027.

Obi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wani taron tattaunawa da al’umma mai taken “Obi Talks Nigeria” da ya gudana a birnin Fatakwal na jihar Ribas, inda ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su hana maimaita kura-kuran da aka gani a zaɓen 2023.

A zaɓen 2023, Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gaza loda sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ta hanyar intanet a manhajar IReV sakamakon abin da ta kira matsalar fasaha, lamarin da jam’iyyun adawa suka yi watsi da shi tare da ƙalubalantar nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kotu, ko da yake kotu ta tabbatar da zaɓen na Tinubu.

Ɗan takarar na NDC ya jaddada cewa waɗanda ke shirin magudi a wannan karon za su fuskanci cikas, yana mai kira ga magoya bayansa da su fito su kaɗa ƙuri’unsu ba tare da fargabar wata barazana ba.

“Babu wanda zai sake tsoratar da mu a rumfunan zaɓe. Idan ka je kowace rumfar zaɓe a yau, mafi yawan jami’an da za ka gani mutum biyar ne, yayin da masu kaɗa ƙuri’a suka kai 40 zuwa 50. Babu yadda za a yi mutum biyar su tsoratar da mutum 50. Wani ya ce ‘a shirye muke mu mutu,’ to bari in gaya muku, ni ma a shirye nake in mutu,” in ji Obi.

Ya ƙara da cewa: “Za mu tabbatar da cewa muna da tsari domin hana duk wata barazana. Za su so yin magudi a manhajar IReV, amma a wannan karon ba zai zo musu da sauƙi ba. Za a samar da hanyoyin bibiyar sakamako da dama a wannan karon. Idan suka ce akwai matsalar sadarwa, za mu kawo musu wanda ba shi da matsala. Barin hakan ya ci gaba zai jefa rayuwarmu cikin garari, wanda shi ne abin da muke fama da shi a yau.”

A nasa ɓangaren, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga masu kaɗa ƙuri’a da su guji maimaita kuskuren baya na rashin zaɓen shugabanni nagari.

Kwankwaso ya jaddada cewa duk da yawan jihohin da jam’iyyar APC mai mulki ke iko da su a yanzu, hakan ba zai hana a kayar da ita ba a zaɓe mai zuwa.

“Ina fatan cewa kada ‘yan Nijeriya su sake yin kuskure. Wannan shi ne lokacin da ya kamata a yi abin da ya dace. Jonathan na kan ƙaragar mulki a matsayin shugaban ƙasa mai ci amma ya faɗi zaɓe. Ina ba da wannan misali ne musamman ga masu tunanin cewa don suna da gwamnoni sama da 30 ba za su iya faɗuwa zaɓe ba. Wannan babban kuskure ne,” in ji Kwankwaso.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata