Hukumomin Iran sun sanar da cewa za a binne tsohon jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, ranar 9 ga watan Yuli a garinsu na Mashhad bayan an jinkirta jana’izarsa sakamakon yaƙin da ya biyo bayan mutuwarsa.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa za a fara gudanar da jana’izar ta kwanaki uku a birnin Tehran daga ranar 4 ga Yuli, kafin a gudanar da wani taro a birnin Qom ranar 7 ga Yuli, sannan a binne shi a Mashhad ranar 9 ga Yuli.
Khamenei ya jagoranci Iran na kusan shekara 37 kafin rahotanni suka ce ya mutu a hare-haren sama da Isra’ila da Amurka suka kai a ranar 28 ga Fabrairu.
Rahotannin sun ce ɗansa, Mojtaba Khamenei, ne ya gaje shi a matsayin jagoran ƙasar a farkon watan Maris. Sai dai tun bayan naɗin nasa bai fito bainar jama’a ba, inda ake cewa yana isar da saƙonninsa ne ta hanyar sanarwar da ake dangantawa da shi.
Ranar 4 ga Yuli da za a fara jana’izar ta zo daidai da ranar bikin cika shekaru 250 da samun ’yancin kan Amurka, kamar yadda rahotannin suka bayyana.
