DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabarai'Allah ne kaɗai zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a Nijeriya'

‘Allah ne kaɗai zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a Nijeriya’

Karamin Ministan Tsaro, Bello Muhammad Matawalle, ya ce matsalar rashin tsaro da ke addabar Nijeriya na buƙatar haɗin kan gwamnati, jami’an tsaro da al’umma baki ɗaya, yana mai cewa Allah ne kaɗai zai kawo ƙarshenta gaba ɗaya.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Matawalle ya bayyana cewa hare-haren ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da ake fuskanta a sassan ƙasar na damun kowa, yana mai kira ga ’yan Nijeriya da su ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro tare da yin addu’ar samun zaman lafiya.

Ministan ya kuma zargi wasu ’yan siyasa da amfani da matsalar tsaro domin cimma manufofinsu na siyasa, inda ya ce bai kamata a mayar da matsalar tsaro wata hanyar cin moriyar siyasa ba.

Ya ce jami’an tsaro na ci gaba da aiki dare da rana domin daƙile ayyukan ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a sassa daban-daban na ƙasar, yana mai jaddada cewa an ba su umarnin ci gaba da murƙushe miyagun laifuka.

Matawalle ya kuma yi zargin cewa ana yaɗa tsofaffin bidiyo da kuma wasu daga ƙasashen waje a kafafen sada zumunta domin nuna kamar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gaza wajen magance matsalar tsaro, yana mai cewa yaƙi da rashin tsaro aiki ne da ke buƙatar lokaci da haɗin kai.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata