Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya mai ɗakinsa, Sanata Oluremi Tinubu, murnar zagayowar ranar haihuwarta inda ta cika shekaru 66 a ranar Litinin, 21 ga watan Satumban 2026.
A cikin wata sanarwa mai cike da kalaman ƙauna da fadar shugaban ƙasa ta fitar a ranar Litinin, Shugaba Tinubu ya bayyana uwargidan tasa a matsayin abokiyar rayuwa wadda ta kasance tare da shi cikin kowane irin yanayi da haƙuri da ƙarfin zuciya.
Tinubu ya kafa hujja da wani karin magana na Yarbawa da kuma littafin Baibul, inda ya bayyana cewa mata tagari ita ce rawanin mijinta. Ya bayyana cewa a tsawon shekarun da suka kwashe tare, Oluremi ta ɗauki duk nauyin da ke kansa, ta kuma kasance tare da shi tana yi masa addu’o’i a lokutan da rayuwa ta kasance cikin tsaka-mai-wuya.
Shugaban ya ce, “Idan har rayuwa za ta maido ni daga farko, to tabbas zan sake zaɓar wannan hanya da ta haɗa ni da ke. A kowane tafarki, zuciyata kullum tana tare da ke.”
Tinubu ya kuma yabawa uwargidan shugaban ƙasar kan ayyukan jin ƙai da ta daɗe tana yi wa al’umma, tun daga gidauniyar New Era Foundation a lokacin da yake gwamnan jihar Legas har zuwa shirin Renewed Hope Initiative a yanzu, wanda ya tallafa wa matasa, zawarawa, tsofaffi, manoma mata, da kuma fafutukar yaƙi da cutar tarin fuka (TB) a faɗin ƙasar.
Daga ƙarshe, Shugaba Tinubu ya gode mata kan gina kyakkyawan gida tare da tarbiyyantar da ‘ya’yansu da jikokinsu, inda ya yi mata addu’ar Allah ya ƙara mata tsawon rai cikin koshin lafiya da farin ciki a sabuwar shekarar rayuwarta ta 66.
