DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 21, 2026
HomeKetareLadanin Masallacin Harami Sheikh Ibrahim Al-Madani ya rasu

Ladanin Masallacin Harami Sheikh Ibrahim Al-Madani ya rasu

Sheikh Ibrahim bin Adel Hamza Al-Madani, ɗaya daga cikin ladanan babban masallacin Harami da ke birnin Makkah (Masjid Al-Haram), ya riga mu gidan gaskiya.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an sanar da rasuwarsa ne da sanyin safiyar ranar Litinin ta shafin dandalin X na ‘Inside the Haramain’, wanda ke kawo labaran masallatai biyu masu alfarma.

Sanarwar ta bayyana cewa kiran sallarsa na ƙarshe a Masallacin Harami shi ne wanda ya yi a ranar Litinin, 11 ga watan Rabi’ul Awwal, 1448 bayan hijira.

Shafin ya wallafa cewa, “Cikin alhini muke sanar da labarin rasuwar ladanin Masjid Al-Haram, Sheikh Ibrahim Al-Madani. Kiran sallar ƙarshe da Sheikh Ibrahim Al-Madani ya yi a Masallacin Harami shi ne na ranar 11 ga watan Rabi’ul Awwal, 1448.”

Za a gudanar da sallar jana’izar marigayin bayan idar da sallar la’asar ta ranar Litinin a Masallacin Harami, kafin daga bisani a binne shi a maƙabartar Al-Mu’alla da ke birnin Makkah.

An haifi Sheikh Ibrahim Al-Madani ne a birnin Madina a shekarar 1397 bayan hijira (1976 Miladiyya). Ya tashi a cikin gidan addini, inda kakan mahaifinsa wanda mahaddacin Alƙur’ani ne ya yi tasiri a kansa tun yana ƙarami.

Yana ɗan shekara 15 ya fara kiran salla a wani masallaci da ke unguwarsu a Madina tare da wasu maƙwabtansu guda uku har zuwa lokacin da ya kammala karatu a kwaleji. Daga baya ya ɗan dakata na wani lokaci sakamakon aikin koyarwa a wajen birnin na Madina.

A shekarar 1428 bayan hijira (2007–2008), ya koma kiran salla a masallacin Masjid Al-Maddah, inda ya ci gaba da aiki har zuwa lokacin da aka naɗa shi a matsayin ladanin Masallacin Harami na Makkah a hukumance a shekarar 1439 bayan hijira (2017–2018).

Sheikh Al-Madani ya samu shaidar karatu a fannin karatun Alƙur’ani (Qur’anic Studies), kuma ya haɗa salo biyu na kiran salla; salon birnin Madina da kuma na birnin Makkah wanda ya koya a wajen Sheikh Abdul Latif Mulla, tsohon ladanin Masallacin Harami kuma aminin kakansa.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata