DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiBBC ta naɗa Haruna Kakangi a matsayin sabon editan sashen Hausa

BBC ta naɗa Haruna Kakangi a matsayin sabon editan sashen Hausa

Kafar yaɗa labarai ta BBC ta naɗa Haruna Ibrahim Kakangi a matsayin sabon editan sashen Hausa na tsawon shekara ɗaya.

Naɗin nasa ya biyo bayan matakai biyu na tambayoyin neman aiki da aka gudanar, inda ya samu nasarar darewa kan wannan matsayi domin jagorantar sashen.

Kafin wannan sabon naɗi, Kakangi ya yi aiki a matsayin babban ɗan jaridar kafafen zaman a sashen BBC World Service.

Kakangi ƙwararren ɗan jarida ne mai kwarewar aiki ta sama da shekaru 10 wajen samar da ingantattun rahotanni ga kafafen yaɗa labarai na duniya.

Sabon editan na da ƙwarewa wajen rubuta labarai masu tasiri, jagoranci, da kuma jawo hankalin masu karatu da sauraro a kafafen yaɗa labarai.

Bugu da ƙari, yana da ƙwarewa ta musamman wajen tsara labarai, tattaunawa, watsa labarai, da kuma dabarun aikin jarida na zamani a kafafen intanet.

Kakangi ya yi karatunsa ne a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga shekarar 2002 zuwa 2008, sannan kuma ya taɓa halartar wata horaswa a cibiyar binciken aikin jarida ta ƙasar Amurka WPI a shekarar 2024.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata