Gidajen mai da dama a faɗin babban birnin tarayya Abuja na ci gaba da ƙara farashin litar man fetur (PMS), a cewar rahoton jaridar Punch.
Wannan sabon sauyin farashin ya biyo bayan ƙarin naira 85 da matatar man fetur ta Dangote ta yi a kan farashinta na sari, inda ya tashi daga naira 1,265 zuwa naira 1,350 a kan kowace lita, a daidai lokacin da farashin ɗanyen mai ke ƙaruwa a kasuwannin duniya.
Wannan mataki yana nuna ƙarin kashi 6.7 cikin ɗari, wanda ya sa farashin sarin matatar ya zarce ainihin kuɗin da ake kashewa wajen shigo da litar man fetur daga waje, wanda a yanzu yake kan naira 1,311 kan kowace lita.
A halin yanzu, ɗanyen mai na Brent, wanda ake amfani da shi wajen auna farashin man Nijeriya, ya kai kusan dala 107.92 kan kowace ganga, inda a yanzu ya ƙara hawa zuwa dala 108.21 a kowace ganga.
Wannan ya ƙara matsa wa ‘yan kasuwar mai lamba tare da haifar da ƙarin sauye-sauyen farashin fetur a sassan Abuja, lamarin da ke nuni da cewa masu ababen hawa na iya fuskantar ƙarin farashi a gidajen mai a makonni masu zuwa, tare da tashin kuɗin sufuri da ƙarin kuɗi ga iyalai.
Binciken da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya gudanar a ranar Lahadi a birnin Abuja ya nuna cewa wasu gidajen mai sun fara ƙara farashin man, inda masu ababen hawa ke biyan ƙarin kuɗi domin samun man.
NAN ta lura cewa gidajen mai na MRS sun ƙara farashin daga naira 1,350 zuwa naira 1,395 a kowace lita, yayin da gidajen mai na NIPCO suka ƙara farashin daga naira 1,350 zuwa naira 1,430 a kowace lita.
Haka kuma gidajen mai na Mobil sun ƙara farashinsu daga naira 1,350 zuwa naira 1,400 a kowace lita. Wata ma’aikaciyar zuba mai a wani gidan mai na MRS, wadda ta buƙaci a sakaye sunanta, ta ce farashin man na iya ƙara tashi daga gobe.
“A halin yanzu muna sayar da tsohon manmu ne a kan naira 1,395 a kowace lita, amma daga gobe, da zarar sabon mai ya iso, farashin zai yi sama,” in ji ta.
Wani masanin tattalin arziki da ci gaban al’umma, Aliyu Ilias, ya bayyana cewa wannan sabon ƙarin farashin man fetur na iya ƙara ta’azzara hauhawar farashin kayayyaki tare da jefa ’yan Nijeriya cikin ƙarin ƙuncin rayuwa.
Ilias ya bayyana cewa hauhawar farashin man fetur zai haifar da ƙarin kuɗin sufuri da na sarrafa kayayyaki, musamman abinci da sauran muhimman buƙatun rayuwa.
“Ina ganin ya kamata a samar da hanyar rage raɗaɗin wannan matsalar. Idan ba a rage raɗaɗin ba, za ta iya bayyana a cikin alƙaluman hauhawar farashin kayayyaki da binciken tattalin arzikinmu na gaba. Yayin da farashi ke ƙaruwa, kuɗin sarrafa kayayyaki zai ƙaru, musamman abinci, domin komai yana shafar kuɗin sufuri. Wannan irin sauyi ba shi da kyau ga tattalin arziki ko kaɗan, kuma mutane za su fuskanci ƙarin wahala a sakamakonsa,” in ji shi.
Tsohon babban sakataren ƙungiyar ƙwadago ta Afirka (OATUU), Mista Owei Lakemfa, ya bayyana cewa dole ne Nijeriya ta kare masu sayen mai daga tasirin sauye-sauyen farashin ɗanyen mai a duniya. Lakemfa ya ce domin yin hakan, ya kamata ƙasar ta ƙarfafa tsare-tsaren tattalin arziƙinta da tsarin dokoki.
A cewarsa, ƙasa irin Nijeriya da ke hako ɗanyen mai kuma take da yawan jama’a, ya kamata ta samar da matakan da za su kare ‘yan ƙasarta daga ƙarin farashin man fetur na ba-zata.
“Tashin hankalin da ke faruwa a tsakanin manyan ƙasashe masu hako mai da masu amfani da shi, da kuma hare-haren da ake kaiwa a Gabas ta Tsakiya, abubuwa ne da za su iya shafar farashin ɗanyen mai a duniya, kuma bai kamata su zama abin mamaki ga mahukunta ba. Mun san cewa rikicin tsakanin Amurka da Iran zai shafi jigilar kayayyakin mai. Mun san da hakan. Tun da muna hako mai kuma muna tace mai a cikin Nijeriya bai kamata mu zama ɗaya da wanda ke shigo da shi ba,” in ji shi.
Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar masu sayar da mai ta ƙasa (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya bayyana cewa ‘yan kasuwa sun sake duba farashin ne sakamakon jerin sauye-sauyen da matatar Dangote ta yi.
Ukadike ya bayyana cewa yawan sauye-sauyen farashin na haifar da rashin tabbas ga ‘yan kasuwa da masu amfani da man, saboda kuɗin sake sayen kayan zai iya canzawa a kowane lokaci.
