An kaddamar da zama na 68 na shugabannin kasashen ECOWAS a cibiyar taro ta fadar gwamnatin Nijeriya, Abuja, ranar Lahadi.
Taron zai mayar da hankali kan musayar ra’ayi na musamman kan makomar kungiyar, da tattaunawa kan muhimman batutuwa na yankin, ciki har da zaman lafiya a siyasa, hadin kai a tsaro, da hade-haden tattalin arziki.
Shugabannin yankin sun isa Nijeriya kafin taron, wanda Shugaban Sierra Leone kuma Shugaban ECOWAS, Julius Maada Bio, ke jagoranta.
A cewar sanarwa a shafinsa na X, Bio ya isa Abuja ranar Asabar don jagorantar zaman, inda ya ce yana fatan tattaunawa mai ma’ana kan kalubalen gaggawa da yankin ke fuskanta, musamman abubuwan da suka shafi Guinea-Bissau da Benin.
