Waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a garin Mokwa na jihar Neja sun shigar da ƙorafi a gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC da hukumar EFCC da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya, suna buƙatar a gudanar da bincike kan adadin kuɗaɗen tallafi da aka karɓa da kuma yadda aka kashe su bayan iftila’in ambaliyar ruwa ta shekarar 2025.
A cikin ƙorafin mai ɗauke da kwanan wata 26 ga Yuni, 2026, wanda kamfanin lauyoyi na I.U. Wali Law Firm ya gabatar a madadin Isah Abubakar (Isah Mokwa), an zargi wasu da karkatar da kayayyakin agaji da kuɗaɗen tallafi tare da rashin gaskiya wajen rabon taimakon da aka tara domin waɗanda ambaliyar ta shafa.
Ambaliyar da ta afku tsakanin 28 zuwa 29 ga Mayu, 2025 ta biyo bayan ruwan sama mai ƙarfi da ya mamaye garin Mokwa, inda ta lalata dubban gidaje, ta yi sanadin mutuwar daruruwan mutane, ta raba dubban mutane da muhallansu, tare da lalata gonaki da dama.
Masu ƙorafin sun ce an tara biliyoyin nairori daga Gwamnatin Jihar Neja, hukumomin tarayya ciki har da NEMA da sauran masu bayar da tallafi, amma da dama daga cikin waɗanda abin ya shafa sun ce ba su samu isasshen taimako ba.
Sun kuma yi zargin an yi maguɗi a jerin sunayen waɗanda suka cancanci tallafi tare da karkatar da kuɗi da kayayyakin agaji.
Masu ƙorafin sun buƙaci ICPC, EFCC da ‘yan sanda su gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana, tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a zargin.
Takardun da aka fitar sun nuna cewa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa sun tabbatar da karɓar ƙorafin.
Wannan mataki na zuwa ne yayin da mazauna Mokwa ke ci gaba da neman cikakken bayani kan yadda aka gudanar da tallafin bayan iftila’in da ya yi mummunar illa ga rayuka da dukiyoyi.
