Nijeriya ce ta zama ƙasa ta daya a Afirka a fannin ƙarfin tattalin arziki, a rahoton World Competitiveness Ranking 2026 da Cibiyar International Institute for Management Development (IMD) ta fitar.
Rahoton ya tantance ƙasashe 70 bisa fannoni huɗu da suka haɗa da ƙarfin tattalin arziki, ingancin gwamnati, yanayin kasuwanci da kuma ababen more rayuwa.
Nijeriya ta samu maki 45.2 a fannin ƙarfin tattalin arziki, inda ta zo ta 55 a duniya, kuma ta zarce sauran ƙasashen Afirka da aka haɗa a rahoton.
Afirka ta Kudu ce ta zo ta biyu a nahiyar da maki 36.27, sai Ghana da 34.6, Kenya da 33.19, Namibia da 22.3, sannan Botswana da 18.25.
Sai dai duk da wannan nasara, Nijeriya ta sauka daga matsayi na 67 zuwa na 68 cikin ƙasashe 70 a jerin ƙasashe mafi ƙwarewa a duniya, inda ta samu maki 38.8.
Rahoton ya danganta koma bayan da matsalolin ababen more rayuwa, ingancin gwamnati da kuma yanayin gudanar da harkokin kasuwanci.
A bangaren ababen more rayuwa, Nijeriya ta zo ta ƙarshe a duniya, yayin da matsayinta ya ragu a fannin ingancin gwamnati daga na 50 zuwa na 53, sannan ta sauka daga na 59 zuwa na 63 a ingancin harkokin kasuwanci.
Sai dai rahoton ya nuna cewa Nijeriya ta yi kyau a fannin tafiyar da kuɗaɗen gwamnati, inda ta zo ta 16, sannan ta samu matsayi na 15 a manufofin haraji.
A ɓangaren tsarin hukumomi da zamantakewa kuwa, Nijeriya ta zo ta 69, yayin da ta samu matsayi na 22 a kasuwar aiki, amma ta kasance ta ƙarshe a duniya wajen sauƙin samun kuɗaɗen jari ga harkokin kasuwanci.
