Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya amince a kai hare-haren sama da Amurka ta yi kan ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar ya ce hare-haren hadin gwiwa ne tsakanin kasashen biyu, inda Najeriya ta bayar da muhimman bayanan sirri kuma an aiwatar da su ne bayan samun cikakkiyar amincewar shugaban kasa.
Tuggar ya jaddada cewa aikin bai sabawa ikon kasa ba kuma ba ya da nasaba da addini.
Gidan talabijin na Channels ya ambato shi ya ce Najeriya kasa ce mai addinai da dama kuma ta na hada gwiwa da abokan hulda irinsu Amurka ne domin yaki da ta’addanci da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.
A cewar Amurka, an kashe ‘yan ISIS da dama a hare-haren, yayin da AFRICOM ta tabbatar da cewa an yi su ne tare da cikakken hadin kai da hukumomin Najeriya.



