Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta kama wani mutum mai shekara 30, Suleman Mamuda, bisa zargin halaka matarsa Umaima Maidawa a unguwar Bayawa da ke Karamar Hukumar Augie ta jihar.
Mai magana da yawun rundunar, SP Bashir Usman, ya ce ana zargin Mamuda da dukan matarsa da sandar iccen fartanya, lamarin da ya yi sanadin ajalinta.
Ya bayyana cewa bayan faruwar lamarin, wanda ake zargin ya tsere daga yankin, amma daga bisani jami’an tsaro suka gano inda yake tare da cafke shi sakamakon bincike da bayanan sirri daga al’ummar yankin.
Rundunar ta ce Kwamishinan ’Yan Sanda, CP Umar Mohammed Hadejia, ya bayar da umarnin mika shi zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) domin ci gaba da bincike da gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.



