Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa Hukumar da ke Yaki da cin Hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, izinin bincike da nazarin na’urorin da aka kwato daga gidan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El‑Rufai.
Alkalin kotun, Joyce Abdulmalik, ta bayar da umarnin ne bayan karar da lauyan ICPC Osuobeni Akponimisingha ya gabatar, inda ya roki kotu ta ba hukumar damar bude na’urorin domin binciken fasaha da fitar da bayanai.
Na’urorin da aka ambata sun hada da wayoyin salula, kwamfuta da kuma na’urorin ajiya na bayanai, inda kotu ta ce ICPC na da hurumin duba sakonnin WhatsApp, kira, hotuna da sauran bayanai domin binciken da take yi.
Sai dai El-Rufai ya shigar da wata kara daban yana kalubalantar binciken gidansa, inda ya bukaci kotu ta bayyana cewa an take masa hakkinsa tare da neman diyya ta Naira Biliyan daya.



