Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiSanata Natasha ta bukaci al’ummar jihar Kogi da su sake sabunta katin...

Sanata Natasha ta bukaci al’ummar jihar Kogi da su sake sabunta katin zabensu

Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi kira ga al’ummar jihar da su yi anfani da wannan lokaci wajen sabunta katin zaɓe da hukumar zaɓe ta kasa ta sanar.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Sanatar ta yi wannan kira ne cikin sakon taya murnar bikin Easter na shekarar 2026, inda ta jaddada muhimmancin haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Ta bayyana cewa sabunta katin zaɓe hanya ce ta ba jama’a damar tsara makomar su ta hanyar zaɓen shugabanni da suke bukata, ta kuma yi kira ga masu jefa ƙuri’a su fito su sabunta katunansu, ko ta yanar gizo ko a cibiyoyin da aka tanada.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata