Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ɗage sauraron yanke hukunci bukatar beli da Hukumar Yaki da Cin Hanci da sauran Laifuka mai zaman kanta (ICPC) ta shigar a kan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
Kotun ta ɗage hukuncin ne daga ranar 14 ga Afrilu da ta sanya zuwa 21 ga Afrilun 2026, bayan da alƙalin kotun, Mai shari’a Dariyus Khobo, ya shiga halin tsaka mai wuya wanda ya hana shi zartar da hukuncin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lauyan wanda ake ƙara, Ubong Akpan, ya bayyana cewa zaman bai ɗauki lokaci ba, inda ya ce suna jiran sabuwar rana domin sanin matsayar kotu kan buƙatar bada belin.
Nasir El-Rufai na fuskantar tuhume-tuhume guda tara da suka haɗa da zargin rashawa da cin zarafin muƙaminsa da almundahana, wanda dukkanin su ya musanta.
A halin yanzu, tsohon gwamnan ya wuce Babbar Kotun Tarayya domin ci gaba da wata shari’a ta daban da ICPC ta shigar akansa.
Lamarin na ci gaba da ɗaukar hankulan jama’a yayin da ake jiran hukuncin kotu kan ko za a ba shi beli ko kuma zai ci gaba da zama a tsare.
