Wani dan jam’iyyar APC Sani Ahmad Zangina, ya yi ikirarin cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na iyakar bakin kokari don ganin ta kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan kasar.
Sani Ahmad ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da DCL Hausa, inda ya yi zargin cewa wasu ‘yan adawa na daukar nauyin masu sukar gwamnatin Tinubu domin a rika ganin rashin kokarinta kan matsalar.
Ya kuma kara da cewa kafin zuwan gwamnatin Tinubu, mafi yawancin ‘yan Arewacin kasar na cikin fargabar yin tafiye-tafiye a mota kan titunan kasar, sakamakon ta’azzarar matsalar satar mutane don neman kudin fansa, sabanin yanzu da lamura suka dauki saiti.
A cewar sa, da al’ummar Nijeriya sun san irin kokarin da gwamnatin Nijeriya ke yi karkashin Shugaba Tinubu, babu shakka za su amince ya yi tazarce a shekarar 2027.
