Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da kafa kwamitin shirya aikin Hajjin shekarar 2026 na jihar, tare da nada Alhaji Ahmad Jafar Jega, tsohon shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Nijeriya a matsayin Amirul Hajj kuma shugaban tawagar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa daga ofishin Sakataren Gwamnatin jihar mai dauke da kwanan wata 9 ga Afrilu, 2026, wadda ta tabbatar da sahalewar Gwamnan kan jerin sunayen mambobin kwamitin.
A cewar sanarwar, an zabo mambobin kwamitin ne daga cikin manyan jami’an gwamnati, masu rike da sarautun gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar.
Kwamitin na da alhakin tsarawa da kuma kula da dukkan harkokin Hajji, tare da hada kai da hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da tafiyar da aikin cikin tsari da nasara.
Haka kuma, an dorawa kwamitin alhakin kula da jin dadin alhazai daga jihar Kebbi a duk tsawon lokacin gudanar da aikin Hajjin.
Daga cikin ayyukan da aka dora musu akwai tabbatar da bin dukkan yarjejeniyoyi tsakanin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar da hukumar NAHCON da kuma kamfanonin jiragen sama.
Haka zalika, za su rika sa ido kan yadda ake gudanar da aikin Hajjin baki daya tare da bai wa gwamnati shawarwari kan yadda za a inganta shi a nan gaba.
