DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, April 21, 2026
HomeLabaraiKotu ta ɗage sauraron belin El-Rufai zuwa watan Yuni

Kotu ta ɗage sauraron belin El-Rufai zuwa watan Yuni

Babbar Kotun Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Darius Khobo ta ɗage sauraron buƙatar beli na tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, zuwa makon farko na watan Yuni, 2026.

Rahotanni sun nuna cewa an ɗage shari’ar ne domin bai wa ɓangarorin da ke shari’a damar kammala wasu muhimman matakai kafin ci gaba da sauraron karar.

Ana tuhumar El-Rufai ne da laifuka da suka haɗa da zargin almundahanar kuɗi da kuma amfani da mukami ba bisa ƙa’ida ba, kamar yadda Hukumar ICPC ta shigar da ƙarar a gaban kotu.

Hukumar ICPC ta ce tuhumar na da alaƙa da wasu matakai da aka ɗauka a lokacin da yake gwamna, wanda ake zargin sun haifar da amfani ga wasu ba bisa ƙa’ida ba.

Ana sa ran kotun za ta yanke hukunci kan buƙatar belin ne a sabon ranar da aka ɗage sauraron shari’ar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata