DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 13, 2026
HomeSiyasaADC ta zargi gwamnatin Tinubu da karkatar da sama da Naira biliyan...

ADC ta zargi gwamnatin Tinubu da karkatar da sama da Naira biliyan 800 domin siyasar 2027

Jam’iyyar ADC mai adawa a Nijeriya ta zargi gwamnatin Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da wasu gwamnoni na jam’iyyar APC da karkatar da sama da Naira biliyan 800 daga kuɗaɗen FAAC domin shirye-shiryen siyasar 2027.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Bolaji Abdullahi ya fitar, inda ta ce zargin cire kuɗaɗen daga asusun rabon kuɗaɗen tarayya domin manufofin siyasa abin kunya ne kuma ya saɓa wa amana. ADC ta ce rahotannin da ke nuna cewa an tara sama da Naira biliyan 800 ta hanyar cire kuɗaɗe daga FAAC ya ƙara tabbatar da zargin da ’yan Nijeriya suka dade suna yi wa gwamnatin APC.

ADC ta ce duk da karin kuɗaɗen da jihohi suke samu bayan cire tallafin mai da kuma sauyin darajar Naira, har yanzu talauci da wahala na ƙaruwa a tsakanin al’umma. Jam’iyyar ta bayyana cewa hanyoyi na lalacewa, asibitoci ba su da kayan aiki, makarantu na fama da ƙarancin kuɗi, yayin da ma’aikata ke korafin ƙarancin albashi.

Jam’iyyar ADC ta yi zargin cewa idan har rahoton da jaridar The Will ta wallafa gaskiya ne, to hakan na nuna ana amfani da kuɗaɗen jama’a wajen gina karfin siyasa kafin zaɓen 2027 maimakon aiwatar da ayyukan ci gaba.

 

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata