Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki na Nijeriya, Saleh Mamman, hukuncin daurin shekaru 75 a gidan yari kan badakalar rashawa da ta shafi ayyukan samar da lantarki na Mambilla da Zungeru.
Mai shari’a Justice James Omotosho ne ya yanke hukuncin a ranar Laraba, bayan kotun ta same shi da laifi a tuhume-tuhume guda 12 da ake masa. Kotun ta bayyana cewa za a aiwatar da hukuncin ɗaurin ne a jere, lamarin da ya kai jimillar shekaru 75.
Kotun ta kuma umarci cewa wa’adin zaman gidan yarin zai fara ne daga ranar da aka kama Saleh Mamman. Haka kuma, Mai shari’a Omotosho ya umarci jami’an tsaro su kamo tsohon ministan a duk inda aka gano shi.
A cewar kotun, dole ne a kwace duk wasu kuɗaɗe da kadarorin da aka karɓo daga hannun tsohon ministan tare da mayar da su ga Gwamnatin Tarayya.
Kotun ta kuma umurce shi da ya dawo da sauran kuɗaɗen da suka rage daga cikin sama da Naira biliyan 22 da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan samar da lantarki na Mambilla da Zungeru.
