DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, May 15, 2026
HomeWasanniManchester United ta amince da Michael Carrick a matsayin kocinta na dindindin

Manchester United ta amince da Michael Carrick a matsayin kocinta na dindindin

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon dan wasan Manchester United Michael Carrick zai ci gaba da zama kocin dindindin na kungiyar bayan shugabannin kulob din sun amince da matakin.

An ce mai kungiyar Sir Jim Ratcliffe ya goyi bayan ci gaba da rike Carrick a matsayin koci, yayin da shi ma Carrick ya amince da sabuwar yarjejeniya da ake shirin kulla masa nan da kwanaki masu zuwa.

Rahotannin sun ce har yanzu ana tantance tsawon kwantiragin, ko zai kasance zuwa shekarar 2028 tare da karin shekara guda ko kuma kai tsaye zuwa watan Yunin 2029.

Carrick, wanda tsohon dan wasan tsakiya ne na Manchester United, ya taba rike kungiyar na wucin gadi bayan tafiyar Ole Gunnar Solskjaer kafin daga baya ya fara aikin horaswa a Middlesbrough.

Magoya bayan United dai na jiran sanarwar hukuma daga kulob din kan sabon matsayinsa da cikakken bayanin kwantiragin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata