Dan wasan gaban Real Madrid, Kylian Mbappé, ya bayyana burinsa na ganin an sake lashe kyautar Ballon d’Or a madadin Real Madrid, yana mai cewa hakan zai ba magoya bayan kungiyar wani dalilin yin murna.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Mbappé ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Diario AS, inda ya ce yana fatan babbar kyautar mutum ɗaya a fagen kwallon kafa za ta dawo Santiago Bernabéu.
Mbappé ya kuma yi magana kan damar da yake da ita ta lashe kyautar, inda ya ce abin da yake yi a fili a filin wasa shi ne ya kamata ya fi maganganunsa bayyana cancantarsa.
Dan wasan na Faransa ya ce yana ganin wannan shekara na iya zama wata dama mai kyau a gare shi ta lashe Ballon d’Or, bayan irin rawar da yake takawa tun bayan komawarsa Real Madrid.
A yayin hirar, Mbappé ya kuma yabawa matashin dan wasan Barcelona, Lamine Yamal, inda ya bayyana shi a matsayin ƙwararren ɗan wasa mai hazaka tare da hasashen cewa zai samu kyakkyawar makoma a harkar kwallon kafa.
Duk da hamayyar da ke tsakanin Real Madrid da Barcelona, kalaman Mbappé sun nuna cewa yana girmama ƙwarewar Yamal da tasirin da matashin dan wasan ke ƙara samu a fagen kwallon kafa.
A yanzu dai Mbappé ya ce babban abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne taimaka wa Real Madrid wajen fafutukar lashe manyan kofuna, yayin da yake kokarin sanya kansa cikin jerin ’yan wasan da ke neman Ballon d’Or.
