DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, May 20, 2026
HomeSiyasaAkpabio da Gwamnoni za su kai labari a zaben fidda gwani na...

Akpabio da Gwamnoni za su kai labari a zaben fidda gwani na Sanatoci?

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, Barau Jibrin, shugaban masu rinjaye, Opeyemi Bamidele; da babban mai tsawatarwa na majalisar Mohammed Tahir Monguno na daga cikin manyan ‘yan siyasar suke fafata wa a zaben fidda gwani na sanatoci na APC da ke gudana yau.

Haka kuma gwamnoni masu ci da ke neman tikitin takarar sanatoci irin su Hope Uzodimma daga Imo ta Yamma, Ahmadu Fintiri daga Adamawa ta Arewa, Abdullahi Sule daga Nasarawa ta Arewa da Mai Mala Buni daga Yobe ta Kudu.

Sauran gwamnoni masu neman kujerar sanatoci sun hada da AbdulRahman AbdulRazaq daga Kwara ta Tsakiya, Muhammadu Inuwa Yahaya daga Gombe ta Arewa da Dapo Abiodun daga Ogun ta Gabas.

Tsofaffin gwamnoni da dama ma sun shiga takarar, ciki har da Yahaya Bello wanda zai fafata da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta jam’iyyar PDP a mazabar Kogi ta Tsakiya.

Hakazalika tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, wanda ke wakiltar Gombe ta Arewa a yanzu, zai kare kujerarsa daga hannun gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin shugabannin majalisar dattawa sun samu tikitin takara ba tare da hamayya ba a yankunansu, yayin da wasu gwamnoni masu ci suka samu maslaha kafin gudanar da zaben fidda gwanin.

Sauran tsofaffin gwamnoni da ke neman kujerun sanatoci sun hada da Jolly Nyame daga Taraba, Simon Lalong daga Plateau da Danjuma Goje daga Gombe.

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, shi ma ya bayyana aniyarsa ta neman takarar kujerar sanatan Delta ta Tsakiya.

Jam’iyyar APC ta fara zaben fidda gwani ne a ranar Asabar da ta gabata da ‘yan takarar majalisar wakilai, yayin da ake sa ran za a gudanar da na sanatoci a fadin kasa yau Litinin.

Jam’iyyar ta kuma kafa kwamitocin sauraron korafe-korafe a jihohi domin karbar koke daga wadanda ba su gamsu da yadda aka gudanar da zaben ba.

A wani bangare kuma, tsohon gwamnan jihar Ogun kuma sanatan Ogun ta Gabas, Gbenga Daniel, ya janye daga zaben fidda gwani na APC saboda zargin shirya tashin hankali a kan magoya bayansa.

A wata sanarwa da kungiyar BATOGD ta fitar, an bayyana cewa Daniel ya umurci magoya bayansa da su kaurace wa zaben saboda barazanar tsaro da ake zargin wasu jami’an gwamnatin jihar na yi musu.

Mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Steve Oliyide, ya tabbatar da matakin, inda ya ce ba za su iya jefa magoya bayansu cikin hadari ba saboda neman tikiti.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata