DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, May 19, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Tinubu ta gaza kawar da matsalar tsaro - Atiku Abubakar

Gwamnatin Tinubu ta gaza kawar da matsalar tsaro – Atiku Abubakar

Madugun adawa a Nijeriya Atiku Abubakar ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Shugaba Tinubu kan yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara, yana mai cewa al’amura sun nuna gazawar shugabanci.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Atiku ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Talata bayan sace ɗalibai da malamai a Ogbomoso da kuma halaka wasu a jihar Katsina.

Atiku ya bayyana damuwa kan yadda aka halaka ɗaya daga cikin malaman makarantar da aka sace a harin Ogbomoso, kuma ya ce hare-haren da ake kai wa makarantu da al’ummomi sun nuna akwai babban gibi a tsarin tsaron ƙasar.

A cewarsa duk lokacin da aka samu irin waɗannan hare-hare, gwamnatin tarayya na fitowa ne kawai da kalaman Allah wadai tare da alƙawarin hukunta masu laifi, amma ba tare da ɗaukar matakan da za su kawo ƙarshen matsalar ba.

Ya kuma ce ‘yan Nijeriya sun gaji da jin irin waɗannan kalamai da ya bayyana a matsayin “tsohuwar magana” wacce ke sanyaya wa mutane gwiwa.

“Atiku ya ce Shugaba Tinubu ya kamata ya daina gudanar da mulki da irin wadannan kalaman, domin rayukan jama’a na ci gaba da salwanta.”

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriyar ya ce masu aikata laifuka sun fara hakan cikin ƙarfin hali saboda sun fahimci cewa ba sa tsoron hukuncin gwamnati ko jami’an tsaro.

Ya ƙara da cewa hare-haren da ake kai wa makarantu, halaka mata masu ciki, da rusa al’ummomi gaba ɗaya na nuna cewa ikon gwamnati ya yi rauni sosai a idon masu aikata laifuka.

Atiku ya kuma nuna damuwa kan zargin da ake yi na cewa ana ƙoƙarin hana yaɗuwar hotuna da bayanan hare-haren domin kada jama’a su ga irin ta’asar da ake aikatawa a wasu yankuna.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata