Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya nuna goyon bayansa ga Ambasada Abdulfatai Yahaya Seriki a matsayin wanda yake son ya gaje shi a zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2027 ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata.
A cikin sanarwar, AbdulRazaq ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tattaunawa mai zurfi da shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki a faɗin jihar Kwara.
Gwamnan ya bayyana Yahaya Seriki a matsayin matashi mai son jama’a, wanda yake da ƙwarewar siyasa da kuma karɓuwa sosai a tsakanin al’ummar jihar.
Ya ce Yahaya Seriki ya taka rawar gani wajen haɗa kan jama’a da kuma zuba jari a harkokin ci gaban jihar, lamarin da ya sa yake ganin ya cancanci jagoranci a wannan lokaci.
AbdulRazaq ya ce ba shi da wata shakka kan cewa Yahaya Seriki na da ƙwarewa da hangen nesa da za su taimaka wajen ci gaba da ayyuka masu alfanu da gwamnatinsa ta fara.
Sai dai gwamnan ya bayyana cewa goyon bayan da ya nuna wa Seriki ba yana nufin hana sauran masu neman takarar gwamna shiga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC ba.
Ya buƙaci shugabanni da mambobin jam’iyyar su haɗa kai tare da tabbatar da nasarar Yahaya Seriki domin ci gaba da haɗin kai da nasarorin jam’iyyar a jihar.
AbdulRazaq ya kuma yaba wa sauran masu neman takarar gwamna bisa nuna dattako da kishin jam’iyya, yana mai cewa dukkaninsu mutane ne masu nagarta da suka cancanci jagoranci.
