Mai bai wa shugaba Tinubu shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, ya tabbatar da cewa kutse a wayar sa da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ambata a wata hira a gidan talabijin gaskiya ne.
Gidan talabijin na AIT ya ruwaito cewa wani shaidar masu gabatar da ƙara daga hukumar tsaro ta DSS ya bayyana hakan a gaban Babbar kotun tarayya da ke Abuja yayin ci gaba da binciken lamarin.
Shaidar DSS ɗin ya ce NSA Ribadu ne da kansa ya tabbatar da sahihancin maganar a lokacin binciken da hukumomi ke gudanarwa kan batun.
Rahotanni sun nuna cewa batun ya samo asali ne daga wata hira da El-Rufai ya yi a wani gidan talabijin, inda ya bayyana ya saurari wayar Ribadu tare da bibiyar wasu tattaunawarsa.
Sai dai bayanan da aka gabatar a kotu sun nuna cewa hukumomin tsaro sun gudanar da bincike kan lamarin, kuma Ribadu ya tabbatar da cewa abinda ake magana akai gaskiyane.
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu sharhi kan siyasa da harkokin tsaro, musamman dangane da batun sirri a harkokin sadarwa da ikon hukumomin tsaro wajen sa ido kan wayoyin mutane.
Wasu na ganin cewa batun na iya ƙara tsananta takun-saƙa na siyasa tsakanin manyan jiga-jigan, musamman bayan tsamin alaƙa tsakanin El-Rufai da wasu masu ruwa da tsaki a gwamnatin Nijeriya.
Har yanzu dai ba a bayyana cikakken bayani kan dalilin sauraren wayar ko kuma irin binciken da ake gudanarwa ba, yayin da kotu ke ci gaba da sauraron shari’ar.
Masana harkokin doka na cewa irin waɗannan batutuwa na da matuƙar muhimmanci saboda suna taɓo batun ‘yancin ɗan ƙasa da kuma ikon hukumomin tsaro.
