Tsohon shugaban Nijeriya Janar Yakubu Gowon mai ritaya, ya yi kira ga ‘yan siyasar Nijeriya su nisanci siyasar “mutuwa ko rai” tare da kawo ƙarshen matsananccin kwaɗayin mulki da ke haddasa rikice-rikice a ƙasar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Gowon ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna My Life of Duty and Allegiance a Abuja.
Tsohon shugaban ƙasar ya ce dole ne ‘yan siyasa su rage sanya damuwa a harkokin siyasa, musamman yadda ake gudanar da zaɓe cikin rashin adalci da gaskiya har ma a zaɓukan cikin gida na jam’iyyu.
Ya bayyana cewa matsalar rashin gudanar da sahihin zaɓe tun daga zamanin mulkin mallaka na daga cikin abubuwan da suka daɗe suna kawo cikas ga cigaban Nijeriya.
Gowon ya ce duk da ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta, yana da cikakken yaƙinin cewa Njjeriya ba za ta rushe ba, yana mai cewa ƙasar ta tsallake manyan ƙalubale ciki har da yaƙin basasa.
Gowon, wanda ya shugabanci Nijeriya tsakanin shekarar 1966 zuwa 1975, ya jagoranci ƙasar ne a lokacin yaƙin basasa daga 1967 zuwa 1970 kafin daga bisani aka hambarar da gwamnatinsa a juyin mulki ba tare da zubar da jini ba.
