DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, May 19, 2026
HomeSiyasaKotu za ta yanke hukunci kan takarar Jonathan

Kotu za ta yanke hukunci kan takarar Jonathan

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 26 ga watan Mayu domin yanke hukunci kan karar da ke neman hana tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Mai shari’a Peter Lifu ne ya dage sauraron karar zuwa ranar bayan kammala sauraron hujjojin lauyoyin mai karar da kuma na wadanda ake kara.

Rahotanni sun nuna cewa wani lauya mai suna Jideobi ne ya shigar da karar yana neman kotu ta hana Jonathan gabatar da kansa ga kowace jam’iyya domin neman tikitin takarar shugaban kasa.

Mai karar ya kuma bukaci kotun ta hana Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) karba, tantancewa ko wallafa sunan Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa.

A cikin karar, Jideobi ya bukaci kotun ta fayyace ko bisa tanade-tanaden sashe na 1(1), (2), (3) da kuma 137(3) na kundin tsarin mulkin 1999, Jonathan na da damar sake neman shugabancin kasa.

Lauyoyin bangarorin biyu sun gabatar da hujjojinsu a gaban kotun kafin mai shari’a ya sanya ranar yanke hukunci.

Ana sa ran hukuncin zai bayyana matsayin tsohon shugaban kasar kan yiwuwar shiga zaben shugaban kasa na 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata