DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, September 27, 2026
HomeKetareAn rantsar da Romuald Wadagni a matsayin sabon shugaban kasar Benin

An rantsar da Romuald Wadagni a matsayin sabon shugaban kasar Benin

Tsohon Ministan Kudi na kasar Benin, Romuald Wadagni, ya zama sabon shugaban kasar bayan an rantsar da shi ranar Lahadi a birnin Cotonou.

Wadagni mai shekaru 49 ya gaji tsohon shugaban kasa Patrice Talon, wanda ya yi mulki na tsawon wa’adi biyu. Ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga Afrilu da kashi 94 cikin 100 na kuri’un da aka kada.

Babbar jam’iyyar adawa ta Democrats ba ta samu damar shiga zaben ba saboda matsalolin amincewa da takardun takara da kuma rikicin cikin gida.

A jawabinsa bayan rantsarwa, Wadagni ya ce zai yi wa kasar hidima cikin gaskiya, jajircewa da kishin kasa.

Ya ce mulki ba wata dama ce ta anfani da kai ba, yana mai alkawarin kare hadin kan kasa da tsaro.

A lokacin da yake Ministan Kudi na tsawon shekara 10, gwamnatin Benin ta samu ci gaba wajen gyara tattalin arziki da rage gibin kasafin kudi zuwa kaso 3 cikin 100 na GDP.

Sai dai duk da ci gaban tattalin arziki, kasar na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro musamman a yankin arewa, inda hare-haren ‘yanta’adda suka karu.

Wadagni ya ce gwamnatinsa za ta dauki matakai masu tsauri domin dakile matsalar tsaro tare da inganta zaman lafiya da kasashen makwabta kamar Nijar da Burkina Faso.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata