Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari wani wajen gudanar da ibada da dare a jihar Kwara, inda suka yi ajalin akalla mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutum 15 a karamar hukumar Ekiti ta jihar.
Rahotanni sun ce harin ya faru ne a daren Juma’a a wani wurin ibada mai suna Ori-Oke Ajaiye da ke wajen kauyen Ikiran a kudancin jihar.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun dira wajen ibadar da misalin karfe 8:30 na dare inda suka fara harbe-harbe kafin su yi awon gaba da wasu masu ibadar zuwa cikin daji.
An ce wadanda aka kai wa harin na gudanar da ibadar dare ne lokacin da maharan suka mamaye wurin, lamarin da ya sa mutane suka rika guduwa domin tsira da rayukansu.
Har zuwa yanzu ba a bayyana sunayen wadanda aka hallaka ba, yayin da ake ci gaba da kokarin gano inda aka kai wadanda aka sace.
Mazauna yankunan da ke kusa da wurin sun ce tsoro ya mamaye al’umma bayan harin, inda suka bukaci gwamnati da jami’an tsaro su kara samar da tsaro a wuraren ibada da kauyukan noma masu nisa.
Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun isa yankin bayan harin tare da fara gudanar da bincike a dazukan da ke kusa domin ceto wadanda aka sace.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta tabbatar da harin ranar Lahadi, tana mai cewa wani Fasto mai suna Adebayo Abiodun ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.
Ta ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ojo Adekimi, ya tura jami’ai na musamman, rundunar PMF da sashen amfani da jirgin sama maras matuki domin gudanar da aikin ceto da kuma cafke wadanda suka kai harin.
Rundunar ‘yan sandan ta bayyana harin a matsayin dabbanci da rashin tausayi, tare da tabbatar wa al’ummar yankin cewa ana ci gaba da kokarin kubutar da wadanda aka sace da kuma kamo maharan.
