Babban hafsan sojin Uganda, Janar Muhoozi Kainerugaba, ya bayar da umarnin rufe manyan kafafen yada labarai biyu mafi girma a kasar, wato Daily Monitor da NTV Uganda.
Kamar yadda Al Jazeera da Reuters suka ruwaito, Muhoozi Kainerugaba wanda dan Shugaba Yoweri Museveni ne, ya bayyana cewa ba za a sake bude kafafen yada labaran ba sai da izininsa.
Hafsan sojin ya bayyana a shafinsa na X cewa bai yarda da ‘yancin kafafen yada labarai ba a Uganda, yana mai cewa daga yanzu dole ne duk wani rahoto mara kyau game da Uganda ya samu amincewa daga ofishinsa kafin a wallafa shi.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro dauke da makamai sun kewaye hedikwatar Nation Media Group da ke Kampala, wanda ke mallakar Daily Monitor da NTV Uganda.
Ma’aikatan kamfanin sun ce an hana shiga da fita daga ofisoshin, yayin da tashoshin NTV Uganda, Spark TV da wasu gidajen rediyo suka daina aiki a sassan kasar.
Muhoozi ya kuma yi ikirarin cewa tun shekarar 2017 mahaifinsa Shugaba Museveni ya ba shi ikon rufe duk wata kafar yada labarai idan ya ga dama.
Muhoozi Kainerugaba na daga cikin mutanen da ake ganin za su gaji mahaifinsa, Shugaba Yoweri Museveni, wanda ya mulki Uganda tun shekarar 1986.
A baya gwamnatin Uganda ta taba rufe Daily Monitor na tsawon kwanaki 10 a shekarar 2013, yayin da aka taba dakatar da NTV Uganda daga aiki a shekarar 2007 bayan korafi kan yadda take yada labarai.
Kungiyar masu gidajen rediyo da talabijin ta Uganda ta bayyana damuwa kan matakin, tana mai cewa hakan na iya yin illa ga ‘yancin fadin albarkacin baki da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
