DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeWasanniYadda kasashen Afirka tara suka kai zagayen ‘32’ a gasar kofin duniya...

Yadda kasashen Afirka tara suka kai zagayen ‘32’ a gasar kofin duniya ta 2026

Kasashen Afirka tara ne suka tsallake zuwa zagayen ‘Round of 32’ a gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026 bayan kammala wasannin rukuni, lamarin da ya sa suka kafa sabon tarihi ga nahiyar a gasar da aka fadada.

Wannan ne karon farko da kasashen Afirka 10 suka samu damar shiga gasar cin kofin duniya a lokaci guda, inda tara daga cikinsu suka samu tikitin zuwa matakin gaba.

Daily Trust ta ruwaito cewa kasashen Morocco, Afirka ta Kudu, Ivory Coast, Masar, Cape Verde, Ghana, Congo DR, Algeria da Senegal ne suka tsallake zuwa zagayen gaba bayan fafatawa da manyan kasashe a gasar da ake bugawa a Arewacin Amurka.

Morocco ta ci gaba da haskawa

Tawagar Atlas Lions ta Morocco ta fara da canjaras da Brazil kafin ta samu nasarar doke sauran abokan karawarta da ci 1-0 domin kare a matsayi na biyu a rukuni na C da maki bakwai.

Afirka ta Kudu ta farfado bayan rashin nasara

Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu ta sha kashi a wasanta na farko da Mexico amma daga baya ta tashi kunnen doki da Czech Republic sannan ta doke Koriya ta Kudu domin tsallakewa zuwa zagayen gaba.

Ivory Coast da Masar sun taka rawar gani

Ivory Coast ta samu nasara kan Ecuador da Curacao duk da shan kashi a hannun Jamus, lamarin da ya ba ta damar zuwa zagayen gaba daga rukuni na E.

Masar kuma ta yi canjaras da Belgium da Iran tare da samun nasara a kan New Zealand, inda tawagar da Mohamed Salah ke jagoranta ta tsallake daga rukuni na G.

Cape Verde ta kafa tarihi a karon farko

A karon farko da Cape Verde ke buga gasar cin kofin duniya, kasar ta tsallake zuwa zagayen gaba ba tare da ta yi rashin nasara ba bayan canjaras da Spain, Uruguay da Saudi Arabia.

Ghana, Congo DR da Algeria sun tsallake daga matsayi na uku

Ghana ta samu tikitin zagayen gaba duk da rashin nasara a hannun Croatia, bayan maki da ta tara a wasannin farko biyu ciki har da canjaras da Ingila.

Congo DR ta samu nasararta ta farko a tarihin gasar cin kofin duniya bayan doke abokiyar karawarta da ci 3-1 domin tsallakewa daga matsayi na uku.

Algeria kuwa ta samu muhimmiyar nasara a kan Jordan sannan ta yi canjaras 3-3 a wasanta na karshe domin samun gurbi a zagayen gaba.

Senegal ta samu tikiti a karshe

Senegal ta fara gasar da rashin nasara a hannun Faransa da Norway, amma daga baya ta farfado da doke Iraq da ci 5-0, lamarin da ya ba ta damar samun gurbi na karshe daga cikin kasashen da suka tsallake a matsayi na uku.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata