Kungiyar Kiristoci ta CAN a jihohin Arewa 19 da Abuja tare da kungiyar Ecumenical Synods of Bishops sun yi watsi da ikirarin Shugaban Amurka Donald Trump cewa sojojin Amurka sun dakatar da kashe-kashen Kiristoci a Nijeriya.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, shugabannin addinin sun bayyana ikirarin Trump a matsayin mara tushe kuma wanda bai dace da hakikanin matsalar tsaron da ake fuskanta a Nijeriya ba.
DCL Hausa ta ruwaito cewa Trump ya bayyana a wani taro da aka gudanar a Washington cewa hare-haren da Amurka ta kai a Nijeriya sun taimaka wajen dakatar da kashe-kashen Kiristoci musamman a yankunan da matsalar ta’addanci ta yi kamari.
Sai dai shugaban kungiyar CAN na jihohin Arewa 19 da Abuja, Reverend Joseph Hayab, ya ce har yanzu ana kashe mutane tare da yin garkuwa da su a sassa daban-daban na Nijeriya.
Ya ce wadanda abin ya shafa ne kadai za su iya tabbatar da ko an samu sauki a matsalar tsaro, ba Donald Trump ba.
A cewarsa, bayan harin da Amurka ta kai a Sokoto a bara, har yanzu hare-haren ‘yan ta’adda na ci gaba a jihohi kamar Katsina da Borno.
“Mutanen da ke hannun ‘yan bindiga a Oyo da Kwara fa? Har yanzu mutane na cikin wahala,” in ji Hayab.
Sakataren kungiyar Ecumenical Synods of Bishops, Archbishop Osazee William, ya ce babu wata gamsasshiyar shaida da ke nuna cewa matakan Amurka sun kawo karshen matsalar tsaro a Nijeriya.
Ya ce abin da mutane ke bukata shi ne cikakken taimako da zai magance tushen matsalar tsaro tare da kare rayuka da dukiyoyi.
William ya kuma nuna damuwa kan rade-radin cewa ana kokarin rage matsin lamba kan wasu batutuwan da suka shafi Nijeriya ta hanyar wasu tattaunawa a bayan fage.
Kungiyoyin addinin sun bukaci gwamnatin Amurka da sauran kasashen duniya su mayar da hankali kan taimako na gaskiya maimakon kalaman siyasa.
Sun ce har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da addabar al’umma a sassa daban-daban na Nijeriya, don haka ana bukatar matakai masu dorewa domin kawo karshenta.
