DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, July 7, 2026
HomeLabaraiAPC na fuskantar kakkausar suka bisa zargin sauya jerin sunayen wasu 'yan...

APC na fuskantar kakkausar suka bisa zargin sauya jerin sunayen wasu ‘yan takara

Ana zargin jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya da sauya sunayen wasu ‘yan takara da suka yi nasara a zaɓen fidda gwani na kujerun majalisar dokoki ta Ƙasa, lamarin da ya tayar da muhawara kan sahihancin tsarin zaɓen ‘yan takarar jam’iyyar kafin babban zaɓen shekarar 2027.

Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyun adawa da dama sun yi martani kan matakin.

PDP ta yi wa APC ba’a saboda maye gurbin wasu da suka lashe zaɓen fidda gwani da wasu, yayin da SDP ta bayyana matakin a matsayin rashin hankali.

Ita kuma jam’iyyar Labour Party ta ce abin ya saɓa wa ƙa’idar dimokuraɗiyya.

Sai dai APC ta buƙaci jam’iyyun adawar su mayar da hankali kan rikice-rikicen da ke addabar jam’iyyunsu, tare da cewa sauye-sauyen sun yi daidai da adalci da kuma muradin mambobinta.

A cewar rahotanni, a makon da ya gabata APC ta umarci rassanta na jihohi su fitar da jerin sunayen ‘yan takararta na zaɓen 2027 tare da fara bai wa ‘yan takara takardun cike fom na Hukumar zaɓe INEC domin gabatar da sunayensu.

Sai dai wasu daga cikin waɗanda aka ayyana a matsayin waɗanda suka yi nasara sun yi zargin cewa an maye gurbinsu ne bayan Kwamitin karɓar ƙorafe-ƙorafen zaɓen fidda gwani na watan Mayu ya kammala nazarin ƙorafe-ƙorafen da aka shigar.

Rahotannin sun ƙara da cewa kwamitin zartarwa na ƙasa na APC ya soke nasarar wasu ‘yan takarar Sanata tare da dawo da tikitin sanatoci shida masu ci a jihohi tara bisa shawarwarin kwamitin ɗaukaka ƙara.

Wannan mataki ya zo ne duk da gargaɗin da INEC ta yi cewa ba za ta amince da sunayen waɗanda ba su fito daga zaɓen fidda gwani da jami’anta suka sa ido a kai ba.

Daga cikin sanatocin da aka dawo da tikitinsu akwai Sunday Karimi, Emmanuel Udende, Titus Zam, Shuaibu Isa Lau da Adeniyi.

Akwai kuma Adegbonmire da Olajide Ipinsagba, yayin da Prince Paul Ikonne ya maye gurbin Edinburgh Erondu a Abia ta Kudu.

Rahotannin sun nuna cewa tsohon gwamnan Jihar Benue, Gabriel Suswam, na cikin manyan waɗanda wannan sauyi ya shafa, bayan da aka soke nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwani na Sanatan Benue ta Arewa maso Gabas Gabas, tare da mayar da tikitin ga Sanata mai ci, Emmanuel Udende.

Wannan mataki ya haifar da sabbin saɓani a cikin APC da tunanin bude sabon babu na shari’a a jihohi da dama da aka gudanar da zaɓen fidda gwani.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata