Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanya ƙasashe 23 cikin matakin gargaɗin tafiye-tafiye mafi tsauri, wato mataki na huɗu (Level 4), inda ta shawarci ’yan ƙasar kada su je waɗannan ƙasashe saboda matsalolin tsaro.
Daga cikin ƙasashen Afirka da ke cikin jerin akwai Burkina Faso, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Chadi, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Libya, Mali, Nijar, Somaliya, Sudan ta Kudu, Sudan da Uganda.
Sauran ƙasashen sun haɗa da Afghanistan, Belarus, Myanmar, Haiti, Iran, Iraq, Lebanon, Koriya ta Arewa, Rasha, Syria, Ukraine da Yemen kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ma’aikatar ta ce ana sanya ƙasa a mataki na huɗu ne idan yanayin tsaro ya yi muni ko kuma gwamnatin Amurka ba za ta iya ba wa ’yan ƙasarta taimako yadda ya kamata ba.
A baya dai Amurka ta sanya Nijeriya a mataki na uku, wato ta bukaci ‘yan ƙasarta su sake nazarin bukatar tafiya zuwa ƙasar saboda matsalolin tsaro, garkuwa da mutane, ta’addanci da rashin kwanciyar hankali.
Sai dai ta ware wasu jihohin Nijeriya cikin mataki na huɗu, ciki har da Borno, Yobe, Jigawa, Filato, Taraba, Neja, Kogi, Kwara, da arewacin Adamawa.
A Kudancin ƙasar kuma, jihohin Abiya, Anambra, Bayelsa, Delta, Enugu, Imo da Rivers, ban da birnin Fatakwal, su ma na cikin yankunan da Amurka ta ce kada ’yan ƙasarta su ziyarta.
Gwamnatin Nijeriya ta mayar da martani inda ta ce wannan mataki na Amurka tsari ne na cikin gida da take bi wajen fitar da irin waɗannan gargaɗi, ba wai yana nuna cewa doka da oda sun rushe a ƙasar ba.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce duk da akwai wasu ƙalubalen tsaro a wasu wurare, Nijeriya na ci gaba da kasancewa ƙasa mai zaman lafiya da kwanciyar hankali.
