DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 22, 2026
HomeBabban Labari Sojoji sun kama wasu 'yan kasar waje da ake zargi da hannu...

Sojoji sun kama wasu ‘yan kasar waje da ake zargi da hannu a matsalar tsaro -Bwala

Mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Daniel Bwala, ya ce dakarun sojin Nijeriya sun kama wasu baƙin haure da ake zargi da hannu a matsalolin tsaro da ke addabar wasu sassan ƙasar.

Bwala ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da aka wallafa ranar Juma’a, inda ya ce gwamnati na gudanar da hulɗar diflomasiyya da ƙasashen da ake zargin mutanen suka fito, saboda haka ba a bayyana ƙasashensu ba.

Ya ce sojoji sun ɓoye bayanan waɗanda aka kama ne domin kada hakan ya kawo cikas ga tattaunawar diflomasiyya da ake yi tsakanin Nijeriya da ƙasashen da abin ya shafa.

A cewarsa, a wasu lokuta ana riƙe irin waɗannan mutane har sai an cimma yarjejeniya tsakanin ƙasashe, ciki har da musayar fursunoni idan ya zama dole.

Bwala ya kuma danganta wasu daga cikin tsoma bakin ƙasashen waje cikin harkokin Nijeriya da muradun tattalin arziki da na tsaro, yana mai tuno da lokacin da aka riƙa daga tutocin Rasha a wasu zanga-zanga a Arewacin ƙasar.

Da aka tambaye shi ko Hukumar Leken Asirin Amurka ta CIA na da hannu wajen ɗaukar nauyin ta’addanci a Nijeriya, Bwala ya ce ba zai iya tabbatar da hakan ba.

Sai dai ya ce wani ɗan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya taɓa tayar da irin wannan batu yayin wani zaman sauraron ra’ayoyi a Majalisar Dokokin Amurka.

Bwala ya ce ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP sun bazu daga Arewa maso Gabas zuwa Arewa maso Yamma, kuma suna ƙoƙarin kutsawa yankin Arewa ta Tsakiya, lamarin da gwamnati ke ƙoƙarin dakilewa.

Ya kuma musanta zargin cewa sojoji na kare ‘yan ta’adda, amma ya amince cewa samun masu ba da bayanan sirri daga cikin hukumomin tsaro abu ne mai yiwuwa.

Bwala ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta gyara matsalolin rashin haɗin kai da ya ce sun taɓa kasancewa tsakanin Sojojin Ƙasa da Sojojin Sama, tare da bayyana cewa gwamnati ta samu ci gaba a fannin tattalin arziki da tsaro.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata