DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, September 23, 2026
HomeWasanni'Yan wasan Nijeriya sun yi zargin sace musu kuɗi a otel da...

‘Yan wasan Nijeriya sun yi zargin sace musu kuɗi a otel da ke Morocco

‘Yar wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta mata a Nijeriya wato Super Falcons, Esther Okoronkwo, ta yi zargin cewa ma’aikatan wani otel da tawagar ta sauka a Casablanca na ƙasar Morocco sun sace kuɗaɗe daga ɗakunan ‘yan wasan kafin fara gasar Kofin Nahiyar Afirka ta Mata (WAFCON) ta 2026.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Okoronkwo ta bayyana hakan ne a wasu saƙonni da ta wallafa a shafinta na Snapchat, inda ta ce kuɗin sun ɓace ne lokacin da ‘yan wasan ba sa cikin ɗakunansu, yayin da ma’aikatan ke aikin gyara ɗakunan. Ta ce da farko ta yi zaton an sace mata dala 500, amma daga baya ta ce bayan ta sake lissafi, asarar ta kai dala 700.

Okoronkwo ta kuma yi zargin cewa wasu ‘yan wasan tawagar sun fuskanci irin wannan matsala. Ta ce Halimatu Ayinde da Asisat Oshoala kowacce ta rasa dala 100, yayin da Joy Omewa ta rasa fam 120. Ta ƙara da cewa sun kai ƙorafi ga jami’an otel, amma ba su samu gamsasshiyar amsa ba.

A cewarta, bayan sun sanar da jami’an karɓar baƙi na otel game da lamarin, ba su nuna damuwa ba. Ta kuma buƙaci mutane su guji sauka a otel ɗin, tana mai zargin cewa ma’aikatansa na satar kuɗin baƙi.

Har zuwa lokacin da aka wallafa rahoton, jaridar Punch ta ce ba ta samu martanin otel ɗin ko na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) kan zarge-zargen ba.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata