Gasannin Premier League ta ƙasar Ingila za su shiga hutun kwanaki 16 na wasannin ƙasashe daga ranar 21 ga Satumba zuwa 6 ga Oktoba 2026, lamarin da zai zama karon farko a tarihin gasar da aka samu irin wannan dogon hutun.
Hakan ya faru ne bayan FIFA ta haɗa hutun wasannin ƙasashe na watan Satumba da na Oktoba wuri guda, kamar yadda Jaridar PUNCH ta ruwaito.
Za a buga wasannin mako na biyar na Premier League har zuwa ranar 20 ga Satumba, kafin a dakatar da gasar, sannan a koma buga wasannin mako na shida daga ranar 10 ga Oktoba.
A lokacin hutun, ƙasashen Turai za su fafata a wasannin UEFA Nations League, yayin da ƙasashen Afirka za su ci gaba da wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka, AFCON.
A wasannin neman gurbin AFCON, kowace ƙasa za ta buga wasanni biyu a cikin wannan dogon hutun.
Kasashen Amurka da Mexico, waɗanda tuni suka samu gurbin shiga zagayen kwata fainal, za su mayar da hankali kan wasannin sada zumunta.
A nahiyar Asiya kuwa, ƙasashe za su buga wasannin sada zumunta domin shirin gasar cin kofin Asiya da za a gudanar a watan Janairun 2027, bayan kammala wasannin neman gurbin shiga gasar.
Haka kuma, wasu ƙasashen Kudancin Amurka za su buga wasannin sada zumunta a lokacin hutun.
A baya, an saba samun hutun wasannin ƙasashe guda huɗu a kakar Premier League, wato a Satumba, Oktoba, Nuwamba da Maris, inda kowace ƙasa ke buga wasanni biyu a kowane hutun.
Sai dai a wannan kakar, an haɗa hutun Satumba da Oktoba, wanda ya mayar da shi hutun kwanaki 16, inda ƙasashe za su buga wasanni huɗu maimakon biyu.
Premier League ta bayyana cewa manufar sauyin kalandar ita ce rage yawan lokutan da ‘yan wasa ke yin tafiye-tafiye daga nahiya zuwa nahiyar domin wakiltar ƙasashensu.
A cewar gasar, matakin zai kuma rage yawan katsewar gasar tsakanin farkon kakar wasa da ƙarshen shekara, daga hutuna uku zuwa biyu.
Majalisar FIFA ta amince da wannan sauyi baki ɗaya a shekarar 2023, inda jin daɗin ‘yan wasa ya kasance cikin abubuwan da aka yi la’akari da su wajen ɗaukar matakin.
Premier League ta kuma bayyana cewa hutun wasannin ƙasashe kan yi wa kungiyoyin gasar Ingila kamar ya fi tsawon lokacin da aka ayyana, saboda ‘yan wasa kan dawo daga tawagogin ƙasashensu amma ba su buga wasa nan take ba sai ƙarshen mako na gaba.
Hutun wasannin ƙasashe na watan Nuwamba zai gudana daga ranar 9 zuwa 17 ga Nuwamba, tsakanin mako na 10 da na 11 na gasar Premier League.
A wannan lokacin, ƙasashen Turai za su ci gaba da wasannin Nations League, yayin da ƙasashen Afirka za su ci gaba da neman gurbin AFCON da wasu wasanni biyu.
Hutun watan Maris kuwa zai kasance daga ranar 22 zuwa 30 ga Maris, tsakanin mako na 30 da na 31 na Premier League.
A watan Maris, wasu ƙasashe za su fara wasannin neman gurbin shiga gasar EURO 2028, yayin da za a buga wasu wasannin zagayen ƙarshe na UEFA Nations League.
An kafa tsarin hutun wasannin ƙasashe na Premier League a shekarar 2002, kuma aka fara amfani da shi wajen wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2006.
FIFA ta samar da ƙayyadaddun lokuta a cikin kalandar wasanni domin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa su kasance cikin shirin sakin ‘yan wasansu domin wakiltar ƙasashensu.
Premier League ta ce manyan gasa irin su gasar cin kofin duniya da gasannin nahiyoyi na iya gudana a cikin wa’adin FIFA, ko da kuwa lokacin ya zo ne a lokacin da gasar Premier League ba ta gudana.
Ta kuma bayyana cewa lokacin da aka gudanar da AFCON tsakanin Disamba da Janairu a kakar wasan da ta gabata, kungiyoyin Premier League sun saki ‘yan wasansu domin shiga gasar, duk da cewa ba a dakatar da gasar Premier League ba.
Rahotanni sun nuna cewa an taɓa tattauna yiwuwar ƙara rage yawan hutun wasannin ƙasashe, amma tsarin da ake amfani da shi yanzu zai ci gaba da aiki aƙalla har zuwa shekarar 2030.
Haka kuma, Premier League ta ce ba a shirya buga wasannin gasar a daren Litinin kafin fara hutun wasannin ƙasashe, ko kuma daren Juma’a bayan dawowar ‘yan wasa daga hutun.
