DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiAPC za ta mutunta yarjejeniyar zaman lafiya a zaɓen 2027 – Tinubu

APC za ta mutunta yarjejeniyar zaman lafiya a zaɓen 2027 – Tinubu

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sake tabbatar da aniyar sa da ta jam’iyyar APC na mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattaba hannu a kai gabanin babban zaɓen 2027.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja, yayin sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta 2027, inda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya wakilce shi.

Shugaban ya yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu da su guji tashin hankali, kalaman ƙiyayya, yaɗa bayanan ƙarya da kuma amfani da bambancin ƙabila ko addini wajen tayar da rikici.

Ya ce APC za ta gudanar da yaƙin neman zaɓenta ne bisa ra’ayoyi, manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar ’yan Nijeriya, maimakon siyasar tashin hankali.

Tinubu ya kuma yi gargadin cewa bai kamata a ɗauki zaɓen 2027 a matsayin wani lamari na “ko a ci ko a mutu” ba, yana mai cewa dukkan ’yan siyasa abokan tafiya ne wajen gina Nijeriya.

Ya ce: “Ko mun yi nasara ko mun sha kaye, Nijeriya ce ya kamata ta kasance babbar mai nasara.”

Shugaban ya kuma yi Allah-wadai da amfani da kafafen sada zumunta da fasahar AI wajen yaɗa ƙarya, tayar da hankali ko neman rura wutar rikici yayin yaƙin neman zaɓe.

Ya yabawa kwamitin zaman lafiya na ƙasa, ciki har da tsohon Shugaban Nijeriya Janar Abdulsalami Abubakar, Sarkin Musulmi da Bishop Matthew Hassan Kukah, bisa gudummawar da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaɓuka.

Tinubu ya kuma bayyana cewa ci gaban amfani da fasaha a harkar zaɓe, musamman PVC da BVAS da INEC ke amfani da su, na daga cikin matakan da za su taimaka wajen inganta sahihanci da amincewa da tsarin zaɓe.

Ya ƙara jaddada cewa bin yarjejeniyar zaman lafiya zai taimaka wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana, gudanar da sahihin zaɓe da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya a Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata