Jam’iyyar ADC ta zargi tawagar yaƙin neman zaɓen Bola Ahmed Tinubu ta 2027 da zama wata mafaka ga wasu mutanen da ke fuskantar tambayoyi kan zargin cin hanci da rashawa a Nijeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa, sakataren yaɗa labarata na ƙasa, Bolaji Abdullahi ya fitar, jamiyyar ta nuna damuwa kan sanya tsofaffin jami’an gwamnati, ciki har da Betta Edu da Ngozi Olejeme, cikin majalisar yaƙin neman zaɓen.
ADC ta ce ya kamata gwamnatin Nijeriya ta bayyana ko an kammala bincike tare da warware zarge-zargen da ake yi wa waɗannan mutane, ko kuma naɗin nasu wata hanya ce ta yi musu afuwa saboda alaƙarsu da APC.
Jam’iyyar ta tunatar da cewa an dakatar da tsohuwar ministar harkokin jin ƙai, Betta Edu, bayan ce-ce-ku-ce kan wani yunƙurin tura Naira miliyan 585 zuwa wani asusu mai zaman kansa.
Haka kuma, ADC ta ambaci tsohuwar shugabar hukumar NSITF, Ngozi Olejeme, wadda ta fuskanci shari’a daga EFCC kan zarge-zargen da suka shafi almundahanar kuɗaɗen gwamnati.
Jam’iyyar ta ce idan har an wanke waɗanda ake zargi daga tuhume-tuhumen da ake yi musu, ya kamata gwamnati ta bayyana lokacin da aka yi hakan, da kuma hukumar ko mutanen da suka gudanar da aikin.
ADC ta kuma zargi gwamnatin da barin wasu binciken laifukan kuɗi su kauce wa idon jama’a, kafin daga bisani waɗanda ake bincika su sake bayyana a wasu muƙaman gwamnati ko na siyasa.
A cewar jam’iyyar, zaɓen 2027 zai kasance wani gwaji ga yadda Shugaba Tinubu ya tafiyar da ƙasar cikin shekaru uku da suka gabata, musamman yadda manufofin gwamnatinsa suka shafi rayuwar ‘yan Nijeriya.
ADC ta ce majalisar yaƙin neman zaɓen APC ba za ta iya kawar da matsalar tsadar rayuwa da talauci da take zargin manufofin gwamnati sun haifar ba.
Jaridar Punch ta kuma ruwaito jam’iyyar ta sake jaddada shirin ta na tallafa wa hanyoyin samar da man fetur ta hanyar wani tsari mai ƙayyadadden kasafi, wanda za a iya bibiyar kuɗinsa da gudanar da bincike a kansa, domin rage farashin man fetur da tsadar rayuwa.
ADC ta ce duk wani tallafi da take ba da shawara a kai zai kasance ƙarƙashin cikakken tsarin sa ido, inda za a iya bin diddigin kowace Naira da kuma tabbatar da yadda ake amfani da kudaden.
A ƙarshe, jam’iyyar ta ce kafin gwamnatin Tinubu ta yi watsi da shirin tallafin da take gabatarwa saboda tsadarsa, ya kamata ta fara bayyana wa ‘yan Nijeriya yadda manufofinta suka jawo ƙarin tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki.
