DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, September 14, 2026
HomeLabarai"Ni ba ɗan APC ba ne, babu abinda zan yi a kwamitin...

“Ni ba ɗan APC ba ne, babu abinda zan yi a kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu” — Wike

Ministan birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ce ba zai iya jagorantar kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu na 2027 ba, saboda ba ɗan jam’iyyar APC ba ne, tare da cewa ba ya son shiga wani matsayi da zai iya jefa shi cikin haɗarin rasa jihohin da yake ganin yana da alhakin taimakawa wajen samun nasara.

Jaridar PUNCH ta ruwaito Wike ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin da yake duba ayyukan wasu manyan tituna a Abuja, ciki har da titin Apo-Karshi da Kubwa-Bwari, bayan fadar shugaban ƙasa ta sanar da kafa kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na 2027 tare da naɗa tsohon Gwamnan Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta-Janar.

Wike ya ce abin da ya fi muhimmanci a gare shi shi ne ganin an samu nasara a wuraren da yake da tasiri, maimakon karɓar wani babban mukami a kwamitin yaƙin neman zaɓe.

Ya bayyana cewa a shekarun baya wasu daga cikin mutanen da suka riƙe matsayin Darakta-Janar na kamfen ɗin shugaban ƙasa sun kasa samun nasarar kare jihohinsu a lokacin zaɓe.

A cewarsa, wasu daga cikin waɗanda suka riƙe irin wannan matsayi sun kasance gwamnoni ko manyan jami’an gwamnati, amma hakan bai hana su fuskantar rashin nasara a jihohinsu ba.

Wike ya kawo misalan zaɓukan 2015, 2019 da 2023, inda ya ce wasu daga cikin Daraktocin-Janar na kamfen ɗin shugabannin ƙasa suka rasa jihohinsu ko kujerunsu a lokacin zaɓe.

Ministan ya ce saboda haka ba ya son ya shiga jerin mutanen da za su mayar da hankali kan jagorantar yaƙin neman zaɓen ƙasa, alhali suna iya kasa samun nasarar siyasa a jihohinsu.

Ya ce yana kallon Rivers da Abuja, a matsayin wuraren da yake da muhimmiyar rawa, kuma abin da yake son mayar da hankali a kai shi ne ganin an samu nasara a waɗannan wurare.

Wike ya kuma jaddada cewa ba ɗan jam’iyyar APC ba ne, don haka a ganinsa ba zai dace ya jagoranci kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ba, duk da cewa yana goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.

Ya bayyana cewa goyon bayansa ga Tinubu ba sai ya zama ɗan APC ba, yana mai cewa tun kafin zaɓen 2023 wasu ‘yan siyasa da ba ‘yan APC ba ne suka haɗa kai domin ganin Tinubu ya samu nasara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata