DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaSauye-Sauyen tattalin arzikin Tinubu rage talauci suke, ba ingiza shi ba -...

Sauye-Sauyen tattalin arzikin Tinubu rage talauci suke, ba ingiza shi ba – Shugaban APC na kasa

Shugaban jam’iyyar APC na Nijeriya, prof. Nentawe Yilwatda, ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa na rage wa ’yan Nijeriya matsin rayuwa ne, ba wai ƙara talauci suke yi ba.

Jaridar The Sun ta ruwaito Yilwatda ya ce cire tallafin man fetur, daidaita tsarin musayar kuɗaɗen waje da sauye-sauyen haraji sun ƙara yawan kuɗaɗen da ke shiga asusun gwamnatoci.

Kazalika ya kuma bukaci ’yan Nijeriya da su riƙa tambayar gwamnonin jihohinsu yadda suke amfani da ƙarin kuɗaɗen da suke samu daga asusun tarayya a wata-wata.

Ya ce sabon tsarin haraji ya ware muhimman abubuwa kamar abinci, ilimi, kiwon lafiya, gidaje da kayan gini daga haraji, yayin da masu ƙaramin kuɗin shiga da ƙananan sana’o’i aka rage musu nauyin haraji.

A cewarsa, hakan na taimakawa wajen rage tsadar rayuwa ga masu ƙaramin ƙarfi da kananan sana’o’i a karkashin mulkin Tinubu.

Yilwatda ya kuma bayyana ayyukan manyan hanyoyi da tashoshin ruwa na zamani da gwamnatin tarayya ke ginawa a matsayin wasu daga cikin matakan da za su bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

Game da zaɓen gwamnan Osun, shugaban APC ya ce jam’iyyar ta samu darasi mai muhimmanci, yayin da ya bayyana zaɓen a matsayin mai zaman lafiya da gaskiya.

Ya ce APC za ta gudanar da bitar cikakken sakamakon zaɓen kafin ta ɗauki matsaya a hukumance nan gaba.

Yilwatda ya kuma nemi afuwar ’yan jam’iyyar da suka ji an ware su ko an cutar da su yayin gudanar da zaɓen fidda gwani da sauran harkokin cikin gida, yana mai cewa APC na buƙatar haɗin kan dukkan ’yan jam’iyyar kafin babban zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata