DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeBabban Labari Sake dawo da tallafin man fetur zai mayar da Nijeriya baya -...

Sake dawo da tallafin man fetur zai mayar da Nijeriya baya – Gwamnatin Tinubu

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na Nijeriya, Mohammad Idris, ya ce sake dawo da tallafin man fetur zai iya mayar da Nijeriya cikin matsalolin tattalin arzikin da ta fuskanta kafin cire tallafin.

Ya ce manufofin gyaran tattalin arzikin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu sun samar da karin kuɗaɗen da za a iya amfani da su wajen ayyukan ci gaba.

Jarida Punch ta ruwaito Idris ya bayyana haka ne a wani bayani da ya fitar cikin wallafar da ya yi a ranar 24 ga watan Agusta, 2026, inda ya ce Nijeriya ta kashe kusan dala biliyan 10 wajen tallafin man fetur a shekarar 2022, a lokacin da samar da ɗanyen mai da kudaden shiga ke raguwa.

Ya ce bayan cire tallafin, an samu albarkatun da suka kai Naira tiriliyan 15.8 tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Disambar 2025. A cewarsa, daga cikin kudaden, gwamnatin tarayya ta samu kusan Naira tiriliyan 5.43, jihohi Naira tiriliyan 6.52, yayin da ƙananan hukumomi suka samu Naira tiriliyan 3.88.

Ministan ya jaddada cewa waɗannan kudade ba sa nufin akwai wani asusun kuɗi na musamman da aka ware a matsayin “kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafi”, sai dai albarkatun da aka saki a cikin tsarin kuɗaɗen tarayya, wanda ya bai wa matakai daban-daban na gwamnati damar ƙara kashe kuɗi kan ayyukan raya ƙasa.

Kazalika ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta kashe kusan Naira tiriliyan 6.47 wajen manyan ayyukan ababen more rayuwa, ciki har da manyan hanyoyi da ayyukan sufuri, gidaje, noma da tsaro. Daga cikin ayyukan da ya ambata akwai babbar hanyar Lagos-Calabar, Sokoto-Badagry da sauransu.

Idris ya ce gyare-gyaren sun kuma ba gwamnati damar ƙara saka jari a harkokin jin daɗin jama’a, inda ya bayyana cewa sama da gidaje miliyan 10 sun amfana da tallafin zamantakewa.

Ya kuma ce an ware sama da naira biliyan 400 ga wasu shirye-shiryen tallafawa jama’a, ciki har da tallafin karatu da lamunin ɗalibai, asusun gidaje da tsarin ba da rance ga masu amfani.

Ministan ya yi gargadin cewa dawo da tallafin man fetur zai iya sake jefa Nijeriya cikin matsin tattalin arziki, ƙarancin man fetur da kuma matsalolin kasafin kuɗi.

Ya ce maimakon a mayar da tsohon tsarin tallafi, ya kamata gwamnati ta ƙara mayar da hankali wajen ganin fa’idar gyare-gyaren ta bayyana a rayuwar talakawa ta hanyar samar da ayyukan yi, inganta ilimi, lafiya, ababen more rayuwa da rage tsadar rayuwa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata