Akalla malamai mata 500 na addinin Musulunci da shugabannin Da’awah daga jihohin Arewa 19 da babban birnin tarayya Abuja ne suka bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda suka amince da sake tsayawa takararsa a karo na biyu a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Matan, karkashin inuwar ‘Muslim Intellectuals Forum’, sun bayyana matsayinsu ne a yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar a Kaduna ranar Lahadi.
Sun ce matakin nasu ya samo asali ne daga abubuwan da suka bayyana a matsayin nasarorin gwamnatin Tinubu a fannonin ilimi, tsaro, samar da ababen more rayuwa da bunkasar tattalin arziki.
Sun bayyana goyon bayan nasu ne cikin wata sanarwar hadin gwiwa da Aisha Iliyasu Tukur daga Jihar Jigawa ta karanta a karshen taron.
Sanarwar ta ce: “Bayan gabatar da jawabai, lura da muhimman batutuwa, yin tambayoyi da kuma doguwar tattaunawa, mahalarta taron sun yi nazari kan alkiblar siyasar kasar nan gabanin babban zaben shekarar 2027.
“Saboda nasarorin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu da kuma manufofinsa, mahalarta taron sun amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya sake yin wa’adi na biyu a matsayin shugaban kasa a zaben shekarar 2027, insha Allah.”
Matan sun ce ci gaba da mulkin gwamnatin zai ba ta damar karfafa shirye-shiryenta, kammala ayyukan da ake gudanarwa da kuma zurfafa sauye-sauyen da aka fara domin inganta jin dadin ’yan Najeriya.
Musamman, sun yaba wa ”Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFund)”, inda suka ce shirin ya kara damar samun ilimi na manyan makarantu tare da rage matsalolin kudi da dalibai da iyalansu ke fuskanta.
A cewar sanarwar, an sanar da matan cewa kashi 70 cikin 100 na wadanda suka amfana da shirin NELFund ’yan Arewa ne, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sun kuma yaba wa matakan da gwamnatin tarayya ta dauka a bangaren tsaro, ciki har da kara sansanonin sojoji, sayen kayan aikin tsaro da daukar karin jami’an tsaro.
Matan sun bukaci gwamnatin Nijeriya da ta ci gaba da fadada shirye-shiryen da take yi a bangarorin tsaro, ilimi, ababen more rayuwa, samar da ayyukan yi da bunkasar tattalin arziki.
Haka kuma, sun yi kira da a kara tuntubar gwamnati da malaman addini, sarakunan gargajiya, shugabannin al’umma, mata, matasa da kwararru.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce goyon bayan da matan suka bayyana wa Tinubu ba ya da alaka da son rai ko wata manufa ta kashin kai, illa dai saboda irin ayyukan da gwamnatin Tinubu ta gudanar.
Sani ya ce matan sun fito ne daga sassa daban-daban na Arewa domin bayyana goyon bayansu ga shugaban kasa bisa la’akari da manufofi da matakan da gwamnatinsa ta dauka.
Ya ce: “Ba su goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda son zuciya ko wasu dalilai na kashin kai. Abin da ya sa suka yi hakan shi ne irin abubuwan da ya yi wa Nijeriya, musamman Arewa; a fannin ilimi, ababen more rayuwa, kiwon lafiya, noma, kuma mafi muhimmanci, a fannin tsaro.”
Gwamna Sani ya bayyana matan a matsayin shugabannin addini masu tasiri, wadanda ke da damar isa ga miliyoyin ’yan Nijeriya a matakin kasa da kasa.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta dauki muhimman matakai wajen bunkasa ilimin zamani, ilimin fasaha da koyon sana’o’i, da kuma shirye-shiryen koyon dabarun dogaro da kai, tare da tallafa wa dalibai ta hanyar NELFund.
Sani ya bukaci matan da su kai sakonsu zuwa dukkan jihohin Arewa 19, kananan hukumomi da mazabu.
Ya kuma bukace su da su mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi manufofi da ayyukan gwamnati a lokacin yakin neman zabe, maimakon amfani da kabilanci, addini ko ra’ayoyin yankuna.
Shi ma da yake magana, shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayyana goyon bayansa ga sake zaben Tinubu, yana mai cewa gwamnonin Arewa da al’ummar yankin za su tsaya tare da shugaban kasar.
Yahaya ya ce halartar mata, matasa, kwararru da sauran masu ruwa da tsaki daga matakin kasa a taron ya nuna muhimmancin hadin kai gabanin zaben shekarar 2027.
