Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Ali Ndume, ya buƙaci jam’iyyun adawa su daina mayar da hankali kan takardun shaidar karatun shugaba Bola Ahmed Tinubu, su karkata hankalinsu wajen tantance ayyukan gwamnatinsa da kuma gabatar wa ’yan Nijeriya da ingantattun manufofin da za su iya bayarwa gabanin zaɓen 2027.
Jaridar Punch ta ruwaito Ndume, wanda jigo ne a jam’iyyar APC, ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar a Abuja ranar Litinin, inda ya ce sake tayar da batun takardun shaidar karatun Tinubu na iya karkatar da hankali daga muhimman batutuwan da ya kamata su mamaye muhawarar neman zaɓe.
Ya ce ya kamata ’yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun adawa su bayyana wa ’yan Nijeriya irin abin da suke da shi na daban, musamman a bangaren manufofin tattalin arziki, tare da nuna abin da za su iya yi fiye da gwamnatin Tinubu.
A cewarsa, abin da ya dace jam’iyyun adawa su yi shi ne su binciki manufofin tattalin arzikin gwamnatin shugaban ƙasa, da kuma yadda gwamnatinsa ta tafiyar da matsalar rashin tsaro tun bayan hawansa mulki sama da shekaru uku da suka gabata.
Ndume ya ce, “Me ya sa takardun shaidarsa za su zama babban abin tattaunawa? Ya kamata su bayyana wa ’yan Nijeriya abin da suke da shi na daban da kuma abin da za su iya yi fiye da shugaban ƙasa.”
Kalaman nasa sun biyo bayan sabon ce-ce-ku-ce da wasu jiga-jigan adawa suka tayar kan bayanan karatun Tinubu a cikin takardar EC9 da aka gabatar wa INEC, bayan da aka lura cewa wasu bayanan makarantun firamare da sakandare ba su cika ba.
Sai dai shugaban ƙasar ya bayyana cewa yana da digirin B.Sc a fannin gudanar da harkokin kasuwanci daga jami’ar Chicago State University, wanda ya samu a shekarar 1979, tare da gabatar da takardar shaidar digirinsa da kuma takardar sallamar bautar ƙasa ta NYSC.
Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce Tinubu ya cika mafi ƙarancin sharadin ilimi da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya gindaya ga duk mai neman kujerar shugaban ƙasa.
Ndume ya yi nuni da sashe na 131(d) na kundin tsarin mulkin 1999, wanda ya tanadi cewa dole ne mai neman takarar shugaban ƙasa ya kasance yana da ilimi aƙalla zuwa matakin takardar shaidar makaranta ko makamancinta.
Ya ce kundin tsarin mulkin bai ce dole sai mutum yana da takardar shaidar sakandare kai tsaye ba, illa dai ya shimfiɗa mafi ƙarancin matakin ilimin da ake buƙata.
