Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya soki matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na barin Nijeriya domin yin hutun makonni uku a wasu ƙasashen Turai.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Obi ya ce Nijeriya na cikin wani yanayi mai tsanani, inda ya bayyana cewa ’yan ƙasa na fama da tsadar abinci da sufuri, yayin da rashin tsaro ke ci gaba da addabar al’umma tare da hana dubban yara zuwa makaranta.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya ce shugaban ƙasa ya kamata ya fi mayar da hankali wajen magance matsalolin da ke addabar ƙasar, maimakon yawan tafiye-tafiyen hutu a ƙasashen turai.
Ya ce shugabanci ya shafi fifita bukatun jama’a, musamman a lokacin da mutane ke fuskantar matsalar ciyar da iyalansu, neman lafiya, ilimi, tsaro da kuma kwanciyar hankali.
Obi ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan yadda Tinubu bai zaɓi yin hutunsa a wani ɓangare na Nijeriya ba.
Inda ya ce yana fatan ganin lokacin da shugaban ƙasar zai iya yin hutu a wurare kamar Kano, Katsina, Sokoto, Cross River, Bauchi da Ebonyi, domin tallata damar yawon buɗe ido da Nijeriya ke da shi ga kasashen duniya.
A cewarsa, yawan zirga-zirgar ’yan Nijeriya da shugabanni a cikin ƙasar zai taimaka wajen bunƙasa yawon buɗe ido, samar da ayyukan yi, ƙarfafa harkokin sufuri, otal-otal, noma, nishaɗi da ƙananan sana’o’i.
Obi ya ce Nijeriya na buƙatar shugabanci da ke fifita ƙasar, mai kula da buƙatun jama’a tare da tsara makoma mai kyau ga al’umma.
