DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeSiyasaZan tura wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye idan na ci zaɓe...

Zan tura wa ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye idan na ci zaɓe – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin cewa zai tabbatar da tura kuɗaɗen da ake ware wa ƙananan hukumomi kai tsaye gare su idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027.

Jaridar Punch ta ruwaito Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Kenneth Okonkwo, ya sanya wa hannu tare da wallafawa a shafinsa na X ranar Talata.

Ya ce gwamnatinsa za ta mutunta kundin tsarin mulki da kuma tabbatar da cikakken ’yancin gudanar da harkokin ƙananan hukumomi.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi nuni da hukuncin Kotun Ƙoli na watan Yulin 2024 kan ’yancin cin gashin kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi, yana zargin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kasa aiwatar da hukuncin.

Atiku ya ce idan aka ba shi dama, gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa kuɗaɗen jama’a sun isa ga matakin gwamnati mafi kusa da su, domin bunƙasa ayyukan raya ƙasa a ƙananan hukumomi, rage talauci da kuma ƙarfafa ƙarfinsu wajen yaƙi da laifuka da ta’addanci.

Ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da barin wasu gwamnoni su ci gaba da iko da kuɗaɗen ƙananan hukumomi saboda la’akari da siyasa, musamman neman goyon bayansu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Atiku ya ce irin wannan tsari bai cancanci Nijeriya ta ci gaba da kasancewa a kai ba, yana mai cewa ’yancin kuɗaɗen ƙananan hukumomi na da muhimmanci wajen tabbatar da ingantaccen tsarin tarayya da kuma kawo ci gaba kai tsaye ga al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata