DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, September 15, 2026
HomeLabaraiKalaman Gwamna Sule cewa 'bai ga ɗan bindiga a hanyar Sokoto ba'...

Kalaman Gwamna Sule cewa ‘bai ga ɗan bindiga a hanyar Sokoto ba’ sun bar baya da ƙura

Ɗan takarar gwamnan jihar Sakkwato a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Manir Muhammad Dan’iya, ya nuna matuƙar damuwarsa kan abin da ya kira yunƙurin jam’iyyar APC na raina ƙalubalen tsaron da ke addabar al’ummomin jihar.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman kan yaɗa labarai ga ɗan takarar, Aminu Abdullahi, ya fitar, inda Dan’iya ke mayar da martani kan kalaman Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, yayin ziyarar da ya kai garin Silame, wanda aka ruwaito ya ce babu matsalar tsaro a jihar bayan shi da kansa ya tuƙa mota daga birnin Sakkwato zuwa garin ba tare da ya gamu da ‘yan bindiga ba.

Dan’iya ya bayyana cewa tafiya a hanya ɗaya lafiya ba zai goge dubban mutanen da suka fuskanci kisa, garkuwa da mutane, raba su da muhallansu, satar shanu, da karɓar haraji ba.

Ya ƙara da cewa haƙiƙanin halin da ake ciki ya fito fili ko a ranar Alhamis, 3 ga watan Satumbar 2026, inda rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato ta tabbatar da kisan mutum biyar da jikkata uku bayan harin da ‘yan bindiga suka kai a Girkau da ƙauyukan da ke maƙwabtaka da su a ƙaramar hukumar Kebbe, kwanaki kaɗan bayan zargin cewa ‘yan bindiga da neman harajin naira miliyan 40 daga mutanen garin Kebbe.

Dan’iya ya tunatar da cewa hare-haren a kwanan nan sun shafi ƙauyuka a ƙananan hukumomin Rabah, Sabon Birni da sauran sassan jihar, inda wani sabon rahoto kan tsaron arewacin Nijeriya ya sanya Sakkwato a cikin jihohin da suka fi fuskantar hare-haren tsaro a watan Agusta, yana mai cewa: “Tambayar ba wai ko Gwamna Sule ya ga ɗan bindiga a tafiyarsa zuwa Silame ba ne; tambayar ita ce ko ‘yan ƙasa suna cikin aminci a gidajensu, gonakinsu, da ƙauyukansu. Amsar ita ce da yawa har yanzu suna cikin matsanancin tsoro.”

Ɗan takarar ya buƙaci Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu, da gwamnatin APC da su fuskanci matsalar da gaske maimakon barin siyasa ta shiga cikin lamarin tsare rayuwar jama’a, tare da kalubalantar gwamnatin jiha da ta bayyana abin da ya faru da tsare-tsaren da ta sha alƙawari na yaƙar rashin tsaro, yana mai cewa: “Kada mu taɓa ɗaukar rashin ganin ɗan bindiga a hanya ɗaya a matsayin rashin matsalar tsaro a jihar.”

A ƙarshe, Dan’iya ya bayyana aniyarsa ta mayar da kare rayuka da dukiyoyi babban aikin gwamnatinsa idan aka zaɓe shi a 2027 ta hanyar tsarin da zai dogara da bayanan sirri da haɗin gwiwar al’umma, yana mai cewa: “Sakkwato ba ta buƙatar wani ya gaya wa mutanenmu cewa suna cikin aminci; mutanenmu suna buƙatar su kasance cikin aminci a zahiri. Dole ne gwamnati ta fara kare rayuka, daga nan siyasa kuma ta biyo baya.”

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata