Jam’iyyar SDP ta ce za ta tsaya takara don neman kujerar shugaban Nijeriya, da kujerun gwamna a jihohi 28, da sauran mukamai a babban zaɓen 2027.
Shugaban jam’iyyar na Nijeriya, Farfesa Sadiq Umar Abubakar Gombe ne ya bayyana hakan a taron ƙasa na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce jam’iyyar za ta kuma nemi kujeru a majalisar dokoki ta ƙasa da kuma majalisun jihohi, yayin da take shirin tunkarar zaɓen.
Gombe ya ce tsarin jam’iyyar a matakin ƙasa, shiyya, jiha, ƙananan hukumomi da mazabu yana nan daram, duk da ƙalubalen da ta fuskanta.
Ya ce jam’iyyar ta ɗauki matakai domin kare haƙƙoƙinta na kundin tsarin mulki da kuma tabbatar da cewa ’yan Nijeriya za su iya amfani da damar kaɗa ƙuri’a ga jam’iyyar SDP.
Gombe ya ce ya kamata a warware duk wani saɓani da ke tsakanin ’yan jam’iyyar ta hanyar tattaunawa da kuma hanyoyin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.
Ya ce SDP yanzu za ta sauya daga matakin ƙarfafa kanta zuwa gangamin neman goyon bayan jama’a gabanin zaɓen 2027, inda za ta ƙara ƙarfafa tsarinta tare da ƙara jan hankalin matasa da mata.
Shi ma sakataren jam’iyyar na ƙasa, Dakta Olu Agunloye, ya ce SDP ta bambanta da sauran jam’iyyun siyasa saboda tana haɗa tsarin siyasa da akidar da take bi.
Agunloye ya ce jam’iyyar ta gudanar da wani tsari na gyaran cikin gida, wanda ya sa ta ƙara ƙarfi, yana mai cewa tana kuma buƙatar samar da cikakken tsari na yadda za ta gudanar da mulki gabanin zaɓen.
Ya ce ’yan jam’iyyar suna da alhakin isar da saƙonta ga ’yan Nijeriya tare da yin aiki domin ganin an zaɓi ’yan takararta.
